Kasuwar Baje-Koli

Kasuwar Baje-Koli Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kasuwar Baje-Koli, Advertising/Marketing, Kaduna South.

TATTALIN ARZIKITattalin Arziƙi (Economy) ya dogara ne a kan samar da Abinci, Sutura, Ayyuka, Kiwon Lafiya, Ilimi, Gine-G...
04/04/2022

TATTALIN ARZIKI

Tattalin Arziƙi (Economy) ya dogara ne a kan samar da Abinci, Sutura, Ayyuka, Kiwon Lafiya, Ilimi, Gine-Gine da sauransu, da kuma rarrabasu, da cinikayyarsu har zuwa ga amfani da su ga al’umma.

Tattalin arziƙi shi ne bunƙasa, aiwatarwa da haɓɓaka ayyukan da ke kawo ci gaban ƙasa, ta hanƴar dogara a kan fitar da amfani daga ayyukan da mutum ke yi don amfanar kansa da kuma kula da su.

Abubuwan da ke haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasa su ne, Mutane, Kasuwanci, Ma’aikatu, da Gwamnati.

Ayyukan tattalin arziƙi ya fara ne tun daga cinikayya, wato a lokacin da mutane biyu s**a ƙulla yarjejeniyar cimma ciniki a kan wani abu da ake so, ta hanyar amfani da kuɗi ko wani abu mai daraja kamar Zinari, Azurfa, Tagulla da dai sauransu, duk da yake ana ganin cinikayya ta kuɗi kawai wani ƙaramin abu ne idan ana magana a kan tattalin arziƙin ƙasa.

Tattali arziƙi, na samun zumma ne tun daga samar da ayyuka ko abubuwan da ke amfani da albarkatun ƙasa ko ma’adinai, aikin Ɗan Adam, da sa jari.

Amma haka ya canja sanadiyyar canjin rayuwa, da kuma ci gaban fasahar Ɗan Adam wurin amfani da injina masu sarrafa kansu, ya kawo samun sauƙi da saurin aikata ayyuka, da kuma rage kuɗin da ayyukan kansa, haka nan kuma samun ci gaba wurin ƙirƙiran sabbin abubuwa, sabbin hanyoyin aiki, sabbin hanyoyin gabatar da ayyuka, Manƴa-manƴan Kasuwanni, kasuwannin da s**a tattari abubuwa daban-daban, ana kuma samun ƙarin kuɗin shiga.

Tattalin arziƙi ya na samun nasara ne sanadiyar ayyukan al’adun al’umma, martabarsu, iliminsu, faɗaɗar fasahar su, tarihinsu, tsarin al’ummar su, tsarin tafiyar da siyasar su da dokokinsu, har wayau da kuma irin yanayin ƙasar, ma’adinan ƙasa, da yanayin rayuwar halittun ƙasar, waɗannan su ne ke bayar da cikkakiyar samun haɓɓakar arzikin ƙasa, kuma waɗannan abubuwan suke bada guri da abubuwan da arziki ke ci gaba da su sannan ya tsarasu a kan anfanuwar ƙasa da al’ummar ta.

Akwai tattalin arziƙi da ya dogara kacokan a kan kasuwanci, kuma ya na gudana ne a kan cinikayyar ayyuka ko kayayyaki tsakanin mutane, ta hanyar samar da su da kai su kasuwanni domin cinikinsu da kuɗaɗe ko dai wani abin da aka ƙayyade mai daraja.

Akwai tattalin arziƙi da ya dogara a kan bayar da umurni daga Ƴan siyasa kaitsaye da kula da yadda ake samar wa ƴan ƙasa da ayyuka ko kayayyaki da kuma yadda za a saidar da su da rarraba su.

Akwai tattalin arziƙi da ya dogara a kan ma’adinan ƙasa, da sanya al’umma a cikin gudanarwar su.

Ƴancin kowacce al’umma ko ƙasa ya dogara ne kacokan a kan bunƙasar Tattalin arziƙi. A yau ƙasar Sin (China) ta fi kowa yawan al’umma amma ta samar da tsarin tattalin arziƙi da kowani ɗan-ƙasa zai sami nagartacciyar rayuwa, da wa su ƙasashe irin Indiya da Amurka da Dubai da Japan da sauran su.

Rashin samar da tsarin Tattalin arziƙi ya haifar da muguwar koma baya ga ƙasashe masu tasowa, hakan ya faru ne saboda sun kasa tsarkake tsarin siyasar su da killace ma’adanai da inganta wutan lantarki da kawo masu zuba jari.

Inganta sana’o’i aba ce da ke da babbar fa’ida, wannan ya na cikin tarnaƙi da ƙasashe masu tasowa ke fuskanta. Wata babbar matsala ita ce, tashe-tashen hankula da muguwar cin hanci da rashawa da ya baibaye su.

Kasuwar Baje-koli
Arzikin ku, a tafin hannun ku !!!

Mene Ne Muhimmancin Hoto A Talla ?A Kasuwanci musamman na Yanar gizo, hoto nada mahimmanci don shine kebawa kwastominmu ...
28/03/2022

Mene Ne Muhimmancin Hoto A Talla ?

A Kasuwanci musamman na Yanar gizo, hoto nada mahimmanci don shine kebawa kwastominmu ku damar ganin hajar da kuka kasa. Har abada Ɗan Adam baya gajiya da hotuna.

Duk abunda ka faɗa, zamu iya tunanin siffar sa a zuciyar mu, ko da ba dai-dai bane.
Amma shi hoto, yana baiwa jama’a Haƙiƙaninin gaskiyar abunda yake faruwa.

Idan kana so ka jawo hankulan jama’a, to ka rinƙa saka hoto mai ma’ana, kuma hoton yayi kyau wanda aka da ɗauka a gidan hoto, ba selfie ba.

Hoto gangariya wanda aka ɗauka a gidan hoto na da matuƙar amfani wajen jawo hankulan jama’a ga sana’ar ka, saboda idan kunne ya ji, to jiki ya tsira.

Ko wacce sana'a kake yi ka tabbatar ka ƙulla alaƙa da masu hoto, ko kasai na'urar ɗaukar hoton (Camera). Don hoto shine abu mafi mahimmanci a kasuwancin yanar Gizo don haka kada kayi wasa.

Kasuwar Baje-koli
Arzikin ku, a tafin hannun ku !!!

Me Ake Nufi Da Tallace-tallace Na Zamani ? Tallace-tallacen zamani wata hanƴa ce da ake amfani da ita don haɓakka Kasuwa...
26/03/2022

Me Ake Nufi Da Tallace-tallace Na Zamani ?

Tallace-tallacen zamani wata hanƴa ce da ake amfani da ita don haɓakka Kasuwanci ko sana'a, da ake amfani da sabon tsari, gurin Samar da ci gaban sadarwa, ko kiyaye halayen mutane don amfanin ɗaiɗaikun mutane da al'umma gaba ɗaya don bunƙasa kasuwanci da tattalin arziki a zamanance.

Sananniyar horo ce a yanzu ana samunta a cikin darussan ilimi, litattafai da kuma hanƴoƴin Sadarwa da yawa, mujallun da bita, tare da shirin yau da kullun na taron Kasuwanci a matakai kala kala harda babban taron kasuwanci na duniya.

Kafofin watsa labarai da kafafen Sada Zumunta na iya zama wani ɓangare na kayan aiki don yin hulɗa tare da wasu masu sauraro, amma bambancin yana da mahimmanci. Ga waɗanda daga cikinmu da ke aiki a cikin tsarin tallace-tallacen zamani wannan yana gabatar da batutuwa masu mahimmanci game da mutunci da tsarin bunƙasa kasuwanci da sana'o'i. Ana buƙatar hanƴar Tallace-tallace na Zamani don warware matsalolin kwastominmu ku na kasuwanci ko sana'a, don ƙara samar da kuɗaɗen shiga da ƙara adadin Kwastominmu ku.

Ta yaya Tallace-tallace Zamani Ya Dace Da Tattalin Arziki ?

A ƙarni na ashirin da ɗaya (21st century's) Kimiyya da fasaha shine yake da tasiri akan duk wata abu da kake don ka rayu, don cikin ƴan shekarun nan da yawa littattafai, ciki har da Nudge, Freakonomics, The Tipping Point, The Spirit Level da cibiyoyin Ilimi da Kasuwanci da dai sauransu, an tsince masu tsara manufofin Kasuwa da masu sana'o'i sun samar da tsarin Tallace-tallace na Zamani don sauƙaƙawa Ƴan Kasuwa. Ana ganin waɗannan a matsayin suna ba da sabbin tunani da hanyoyin magance canjin ɗabi'a da rashin daidaito tsakanin abokan hulɗar Kasuwanci.

Hakan na baka damar ƙalubalantar kishiyoyin ka na kasuwanci da bada amsoshi ga wasu ƙalubalantar ka, hakan na baka damar fuskantar al'umma da hajar da ka kasa.

Waɗannan suna ba da ra'ayi na al'umma ta hanyar ma'auni na tattalin arziki, wanda ke ƙoƙarin magance gazawar al'ada, ko tattalin arziki na zamani, tare da ƙarin mahimmanci ga fahimta da kuma ra'ayi na tunani na sau da yawa halin rashin hankali na mutane da ƙungiyoyi .

Don haka, masana tattalin arziƙi na ɗabi'a suna ƙara ganin fifikon kasuwancin Zamani akan ƙa'idar ɗabi'a a matsayin babban kayan aiki don magance batutuwa da yawa.

Wajibi ne mu tabbatar mun inganta kafafen Sada Zumunta misali :- Facebook, Twitter, WhatsApp, Telegram, Instagram da YouTube da sauransu.

Adireshin Imel (Email) da saƙon karta kwana (SMS) da ƙirƙirar shafin yanar gizo (website) da zane-zane (Graphics) mai inganci da hotuna masu kyau da Allon Talla (Bill Bord) da sauran su.

Kasuwar Baje-koli
Arzikin ku, a tafin hannun ku !!!

Menene Cinikayya ?Da farko dai cinikayya (trading), a wajen ƴan Crypto, tana nufin saye da siyarwar kadara ko haja (asse...
25/03/2022

Menene Cinikayya ?

Da farko dai cinikayya (trading), a wajen ƴan Crypto, tana nufin saye da siyarwar kadara ko haja (assets).
Idan ka siya kayan abinci a kasuwa ko kuma a shago, wannan ana kiranshi cinikayya. Idan ka canja tsohuwar wayarka ta salula aka baka sabuwa, shima wannan ana kiranshi cinikayya.

Atakaicen takaitawa, duk wani aiki da zaka bada wani abu ga wani mutum domin ya baka wani abu a maimakon sa, sunan wannan cinikayya (trade).

Wannan ƙa’ida takai har cikin kasuwannin cinikayyar kuɗaɗe (financial markets). Zaka iya cinikin
kadarar kuɗi kamar hannun jari da bada lamuni da canjin kuɗi da cryptocurrencies da sauransu.

Ire-iren Cinikayya.

- Scalping
- Day Trading
- Swing Trading
- Positional Trading

Cinikayyar sauri (Scalping) Cinikayyar sauri tana faruwa cikin ƙaramin lokaci.
Masu cinikayyar sauri (Scalpers) suna amfani da ƙaramar juyawar farashi cikin sauri, sau da yawa suna shiga kasuwa su kuma fita acikin mintuna (ko kuma sakanni).

A mafi yawan lokuta, suna amfani da nazrin lissafin kasuwa (technical analysis) a ƙoƙarinsu na hasashen juyin da kasuwa zata yi sannan suyi amfani da Jadawalin kasuwa da kuma
wasu naƙasoshin na kasuwa, domin samun riba. Saboda ƙarancin lokaci, masu cinikayyar sauri suna sauri suna bin ƙaramar riba ne, sau da yawa ƙasa da kaso ɗaya bisa dari (less than1%).

Amma cinikayyar sauri wasa ne na lambobi, maimata samun ƙaramar riba zaisa su taru cikin lokaci. Kasuwancin
nan ta ko wace hanƴa ba na karamin masanin kasuwa bane.

Fahimtar ilimin
kasuwa mai yawa, Dandamali (exchanges) da kake cinikayya akai, da kuma ilimin nazarin lissafin kasuwa sune hanƴoƴi masu matuƙar amfani wajen fahimtar cinikayyar sauri.

Cinikayyar Dogon Lokaci (Swing Trading).

Masu cinikayyar Dogon Lokaci (Swing Traders) suna amfani da lokuta masu tsawo suna riƙe kasuwa
kowanne lokaci daga kwana biyu zuwa watanni.

Burin dai shi ne cin riba mai yawa ta dalilin babban juyin kasuwa "swings“ ko kuma juyin farashi.
Sau da yawa, burinka a matsayin mai cinikayyar dogon lokaci shi ne gane coin da bashi da daraja sosai wanda kuma ake tunanin a gaba zai iya yin daraja.

Daga nan sai ka siya wannan coin ɗin, sai kuma a siyar dashi a lokacin da ya tashi, domin samun riba. Ko kuma, zaka iya ƙoƙarin neman wanda yake da daraja sosai wanda kuma ake sa ran zai sauka a nan gaba.

Hakanan kamar yadda yake da cinikayyar rana, masu cinikayyar dogon lokaci da yawa suna amfani da nazarin lissafin kasuwa.

Bugu da ƙari, yayin da tsarinsu ya lalace a tsawon lokaci, nazari na musamman (Fundamental Analysis) yana zame masu abin dogaro maimatuƙar amfani. Kamar dai yadda baya zuwa
da takura da firgici na cinikayyar rana ɗaya. Cinikayyar dogon lokaci zai iya zama mafi dacewa ga wadanda basu ƙware ba.

Cinikayyar rana ana alaƙanta ta ne da saurin yanke hukunci da kuma bata lokaci mai yawa wurin duban
sikirin (screen), cinikayyar dogon lokaci zata baka damar yin amfani da lokutan ka yayinda kuma
kana cikin cinikayyar.

Cinikayyar rana daya (Day Trading).

Cinikayyar Rana ɗaya ita ce zaka gani da yawa a fina-finai da s**a ƙunshi masu kasuwar hannun jari (Wall
Street).Tsarin cinikayyar rana ɗaya ya ƙunshi shiga da fita daga cikin kasuwa acikin rana ɗaya.

Kasuwannin Cryptocurrencies, idan kun kula, basu da lokutan rufewa ko buɗewa. Zaka iya cinikayyar a cikin duk sa'a ashirin da hudu na rana a duk shekara.

Haka zalika, Cinikayyar rana a gurin cryptocurrency ana nufin wani irin tsarin cinikayya ne inda mai ciniki zai shiga ya kuma fita daga kasuwa acikin sa'a ashirin da hudu. A cikin cinikayyar rana ɗaya, sau dayawa zaka dogara ne da nazarin lissafin kasuwa wurin fitar da hajar da ya
kamata kayi kasuwancinta.

Saboda riba acikin ƙaramin lokaci kaɗan ce, zaka iya zaɓar cinikin coins masuyawa mabanbanta domin ƙoƙarin habaka riba. Wannan yana nuna cewa, wasu zasu iya cinikayyar coins iri
ɗaya aduk shekarar.Wannan tsari a bayyane yake cewa shi ne tsari mafi zama aikin dake bukatar kuzari.

Zai iya zama yanada riba mai yawa, amma kuma ya ƙunshi kasada sosai. Haka zalika, cinikayyar rana tafi dacewa da ƙwararru (experienced traders).

Saka Jari (Positional trading or Investing).

Saka Jari yana aiki da lokaci mai tsawo (LTF) a wurare, ko kuma cinikayyar da aka saka Jarin (positions) a lakuta
da dama ana riƙe su ne daga wata uku zuwa shekara biyar koma fiye da haka. Saka Jari yana ajiye kuɗi na dogon lokaci. Mafi yawan lokuta, mai saka jari yana amfani da Nazarin Kasuwa na musamman (FA) da kuma Nazarin lissafin Kasuwa kaɗan, wani lokacin ma basayi.

Sau da dama, muradin ka/ki a matsayin Mai Saka Jari shi ne fitar ko gane coin ɗin da yake da ƙarancin daraja wanda da alamu zaiyi daraja. Zaka siya wannan hajar ko coin ɗin, sai kuma ka siyar idan ya tashi. Saka Jari yafi dacewa da wanda bashi da Ilimi sosai, ma’aikatan Gwamnati da Likitoci da Lauyoyi da kuma ɗalibai. Yanzu abin tambayar shi ne, wace irin cinikayya
ce kasuwa tafi dacewa da kai?

©Abubakar Salisu Abubakar

Yadda Ake Rubuta Tsarin Sadarwa A Kasuwanci. Ga wasu matakai da ya kamata Kowani Ɗan Kasuwa ko mai sana'a yabi  domin ru...
24/03/2022

Yadda Ake Rubuta Tsarin Sadarwa A Kasuwanci.

Ga wasu matakai da ya kamata Kowani Ɗan Kasuwa ko mai sana'a yabi domin rubuta ingantaccen tsarin sadarwa na Kasuwanci.

1. Gudanar da binciken kayan sadarwar ku, wanda yayi daidai da Sana'ar ku ko Kasuwanci ku.

Kafin wani kamfani ya yanke shawarar rubuta wani shiri, ya kamata yasan inda za a yi amfani da shi ga kasuwancin. Yana da mahimmanci gudanar da binciken yanayin sadarwa na lokacin da ake ciki, a cikin Masana'antar ku. Yana taimakawa wajen gano abubuwa da ke cikin kasuwancin.

Yana taimakawa wajen gano matsalolin ku da kuma gazawar ku da ke cikin Kasuwancin.

Acikin taswira na Kasuwanci ku wajibine ku samar da dama ga wanda zaku nufa da Kasuwancin ku don yi masu Tambayoyi don sanin abinda suke so da wanda basaso hakan zai ƙara inganta tsarin sadarwa a kasuwancin ku.

2. Tsarin Sadarwa Na SMART.

Don yin shirin sadarwa, saita manufofin SMART kamar yadda sakamakon binciken ku zai zama mataki na gaba a Kasuwanci .

Ku kwatanta wasu manufofi bincike da kuka samu dangane da sakamakon kuka samu a baya hakan zai baku cikakkiyar dama ta kasuwanci.

Ya kamata kuyi la'akari da cewa burin da kuke so ko manufofin kasuwancin ku, wajibine ayyukan da kukeyi su zama suna tafiya akan manufar da kuka tsara kasuwancin ku, kowane kasuwanci yana da kyau ya dunga tafiya akan burin da aka ɗora shi akai. Wajibini a samar da tsarin sadarwa wadda ya dace da Manufar Kasuwancin da aka kai.

Hakan na nufin idan har kasuwancin da ake yi bata san abin da suke fatan cinma buriba , ba za su taba cimma burinsu ba. taron da aka shirya don wannan kasuwancin inda za a rubuta maganganun da s**a dace don bayyana manufofin ba tare da wata shubuha ba.

3. Gano masu sauraro don isar da tsarin sadarwar ku

Kyakkyawan tsarin sadarwa ya shafi sauraron mai sauraro, wato, mai da hankali kan masu sauraro. Bayan kafa da gano manufofin, wata kasuwanci na bukatar tantancewa da bayyana masu sauraronta. Yana iya zama ma'aikatan kamfanin, masu hannun jari, kafofin watsa labarai, da dai sauransu.

Isar da kwastomomi na yanzu don koyon abubuwan da suke so. Wani kamfani zai iya amfani da kayan aiki kamar Google Forms ko SurveyMonkey don tattara bayanai daga masu sauraronsu. tattara ainihin bayanan da suke nema.
Shiga cikin Google Analytics don ƙarin koyo game da wanda ke ziyartar shafin yanar gizon kamfanin a halin yanzu.
Kwatanta mabiya fafatawa a dandalin sada zumunta tare da abokan Kasuwancin mu da kuma ganin nau'in mutanen da ke biye da su.
Bayan tattara bayanai ta hanyar da ke sama, wani zai tsara wani zaɓi don bayanin layi ɗaya zuwa biyu na masu sauraro.

4. Tsarin Sadarwa Na Outline Audience.

Bayan gano masu son sauraro, lokaci ne da Kasuwancin za ta bayyana duniya game da kanta. Don haka, akwai buƙatar wani kamfani ya fayyace tare da shirya tsarin sadarwarsa.

Hanya mafi kyau ita ce ƙirƙirar taswira da cika bayanan da s**a shafi saƙonnin da kamfanin ke son tallatawa, masu sauraro da aka nufa da halaye ko tashoshin da za a karɓa. Bayan samar da wani sha shi, da waɗannan

Manufa (Saboda wane dalili aka shirya tsarin sadarwa)
Tsarin Tsinkaya (gami da 'layin farko na tsaro da ƙungiyar amsawa mafi girma')
Matsayin ayyuka da nauyin da aka sanƴa wa kowane
Wani tasiri mayar da martani shirin
Yayin rubuta tsarin sadarwa, aiki tare da ƙungiyoyi na Kasuwanci ko wakilai na masu ruwa da tsaki na Masana'anta na taimakawa wajen inganta daidaito. Dabarun AIDS a warware matsalar shirin kasuwancin da aka nufa.

5. Ƙayyade Tashoshi Don Raba Tsarin Sadarwa.

Tashoshin da Masana'anta za ta amince da su sun dogara ne da saƙon da za a isar da kuma masu sauraron da aka yi niyya game da saƙon.

Ya kamata wata kowacce Masana'anta ta ƙayyade hanƴoƴin kayayyaki game da manufofinta da ke da nasaba da shirinta na sadarwa. Wasu daga cikin hanƴoƴin da kamfanonin s**a fi amfani da su su ne:

- kafa wani Blog
- Samar E-mail na Kasuwanci
- Kafafen Sada Zumunta na Zamani (Social Media) Marketing
- Aika saƙon karta kwana (SMS Marketing)
- Kafofin watsa labarai. Redio da TV da Jaridu da Mujallu
- Talla na Podcast
- Pliers da Banners
- Sai tsarin Talla na Gargajiya.

6. Yanke Shawarar Wani Ɓangare Ne Ke Da Alhakin Isar Da Saƙon Kasuwanci ?

Bayan ƙayyade tawagar da alhakin isar da manufofin da kuma saƙonsu ga duniya.

Misali, idan KBK ta Kamfanin Life Trust ne tana haifar da sabon ci gaba zuwa ga jagoranci, yana iya tambayar Daraktan KBK don isar da filin farko a taron.

Wakili da zai ba da horo d ga kowace kasuwanci a cikin gida wajibine a tabbatar da cewa kowane ma'aikaci a kamfanin ya san abin da ke faruwa a ciki kuma sun san dalilai a bayansa.

7. Ƙiyasta Lokacin Kowane Mataki Na Tsarin Sadarwa.

Misali, ga ƙaramin yaro a cikin kamfanin talla, sashen talla na iya kimanta sake zagayowar don magance matsalar zai ɗauki wata ɗaya wanda zai iya haɗawa da tarurruka
tare da abokin ciniki, masu ruwa da tsaki, da sauran ma'aikata don tattauna ƙarin matakai.

8. Auna Sakamakon Shirin Sadarwa.

Ya kamata ku auna sakamakon shirin sadarwa don hakan zai ɗaga darajar kasuwancin ku.

Auna kowane zaren guda na kamfanin aiki ne mai mahimmanci don samun ra'ayi da nazarin aikin kowane sashen, wanda ya cimma hakan burin da ake so, wanda sashe ke buƙatar ƙarin kuɗi ko ma'aikata don inganta ingancinsa.

Ma'aunin sakamako ko sakamako ya dogara da hanyoyin da kamfani ya bi. Yana taimakawa wajen samun rahoton kowane sashen na kamfanin, gano ramukan, da kuma yin aiki daidai da inganta aiwatar da ayyukan.

Kasuwar Baje-koli
Arzikin ku, a tafin hannun ku !!!

SANA'O'IN MUSana'ar sai da turare ta jima a ƙasar Hausa da ma Najeriya baki ɗaya. Sana'a ce mai albarka da kuma samar da...
23/03/2022

SANA'O'IN MU

Sana'ar sai da turare ta jima a ƙasar Hausa da ma Najeriya baki ɗaya. Sana'a ce mai albarka da kuma samar da rufin asiri ga duk mai yin ta.

Haƙiƙa wannan sana'a ta kasance sananniya a yankin Arewa maso gabas, yankin da aka santa da sarrafa turaruka kala-kala. Masu sai da turare su na burge mutane da al'adar su na shafawa jama'a turare a duk inda s**a taru koda kuwa ba za su siya ba.

Me ya fi ba ku sha'awa dangane da wannan sana'ar?

Tayaya za'a zamanan tar da ita?

Kasuwar Baje-koli
Arzikin ku, a tafin hannun ku !!!

Nazari Akan NomaNoma ya na da ma'anoni da dama kasancewar irin amfanin sa a fannoni daban-daban. To amma dai a fassara m...
22/03/2022

Nazari Akan Noma

Noma ya na da ma'anoni da dama kasancewar irin amfanin sa a fannoni daban-daban. To amma dai a fassara mafi sauƙi, zamu ce, Noma wata hanyar sana'a ce domin samun abinci da kuɗin shiga.

Haka zalika, noma wata babbar hanƴa ce ta samun ƙaruwar tattalin arziki da al'umma s**a raja'a a kan ta.

A ƙasar Hausa, noma ita ce babbar hanƴa ta samun haɓakar tattalin arziki. Da noma ne hausawa s**a fi samun kuɗin shiga da abinci dama kayayyakin da ake sarrafawa a masana'anta kamar tufafi da sauran su. Ba Hausawa kaɗai ba harda sauran Al'ummoni daban daban na duniya.

A wajen Hausawa musamman mazauna karkara noma ta zama kamar wajibi (dole) a wajen kowanne bahaushe musamman magidanci.

Kusan mu ce ma ko wanne bahaushe ya iya noma ya san yarda ake yin ta. Noma da Kiwo duk ta na nufin abu guda ne.

Amma a ƙarni na ashirin da ɗaya (21st century) Kimiyya da Fasaha ya kawo gagarumin sauyi da cigaba ciki harda noma da kiwo. An sami tsarin noman Zamani da yake samar da ɗinbin kuɗaɗen shiga ga Al'umma ta hanƴar Kimiyya da fasaha cikin sauƙi da biyan buƙata. Ƙasahe irin su America da Brazil da Russia da China da Ingila da sauran su, inda tuni s**a yi nisa akan noman Zamani wajen bunƙasa Tattalin arzikin kasashen su.

Ku biyo mu a karo na gaba In Sha Allah zamu haɗu daku a akan Noman Zamani (Machnise Farming).

Kasuwar Baje-koli
Arzikin ku, a tafin hannun ku !!!

Mene ne Tsarin Sadarwa? Ma'anar sa Da Muhimmanci Sa A Kasuwanci ? Ma'anar - Tsarin sadarwa yana bawa ƙungiya ko kasuwanc...
21/03/2022

Mene ne Tsarin Sadarwa? Ma'anar sa Da Muhimmanci Sa A Kasuwanci ?

Ma'anar - Tsarin sadarwa yana bawa ƙungiya ko kasuwanci damar tsara taswirar hanƴoƴi don isar da saƙƙoni ga masu sauraron da aka nufa. Tsarin sadarwa yana bawa ƙungiyoyi ikon aika saƙo da sakamako tare da saƙon yaje gurin wanda aka nufa musamman tallata hajarsa na Kasuwanci.

Wannan zai sa harkokin kasuwanci su samu cikakkiyar fahimta yadda za su faɗaɗa isar su tare da saduwa da masu sauraron da s**a dace da saƙonnin su.

Don haka, idan kuma kuna buƙatar sanin wani shiri ya kamata ya haɗa a cikin samfurin tsarin sadarwar ku, to wannan saƙon zai bankaɗo rawar da shirin sadarwar zai taka wajen gudanar da aikin, hulɗar jama'a,
Da sadarwa da tsarin Kasuwanci a zamanance kuma ya warware maku matsalolin ku. Don haka, bari mu fara .

Mene ne Tsarin Sadarwa?

Tsarin sadarwa hanya ce da aka tsara manufofi wanda ke taimakawa wajen isar da bayanan yadda ya kamata ga masu ruwa da tsaki mu musamman Abokan hulɗar Kasuwanci da Kwastominmu ku.

Musamman, shiri ne na ƙarshe zuwa ƙarshe don isar da bayanan dabaru ga masu sauraro da ake so don haɓaka sakamakon kasuwanci. kungiyar da kake ƙoƙarin kai wa, saƙon da za a tura a can da kuma hanyoyi ko hanƴoƴin sadarwa da za a sa don isa gare su yadda ya kamata.

Ya kamata a dunga bincike na bayanan sirri akan kowacce kasuwanci ko sana'a ake yi don hakan zai baka dama, ku a tsara yadda za'a watsa su don inganta kasuwanci da hulɗa da Kwastominmu ku na kasuwanci.

MUHIMMANCI

Waɗannan na daga cikin muhimman abubuwan da ke nuna bukatar tsare-tsaren sadarwa a Kasuwanci.

1. Bayyana manufofi da burin Kasuwanci ku.

Idan aka yi la'akari da shiri a matsayin taswirar hanƴa, wani tsayayye ya san mene ne wurin da za a nufa, kuma mecece manufar da ake so a Kasuwanci ko Sana'o'i hakan zai baku damar da inganta sana'ar ku da Kasuwanci ku.

Rawar da shirin sadarwa ke takawa domin warware maku matsalar kasuwanci ko fayyace manufofin
na Sana'o'i da kukeyi.

2. Ƙayyade dangantaka tsakanin masu sauraro ko bibiyar kafafen sadarwa na kasuwanci ku, ko abokan hulɗar kasuwanci ku.

Mayar da tsare-tsaren sadarwa zai taimaka waje samar da tsayayye ko gano wanda yake son ya kai, ya sanar da su irin bayanan da yake son fitarwa daga gare su da kuma hanƴoƴin da za su kai gare su don ƙara adadin masu buƙatar kayan da kuke yi.

Kamfanin zai gano cewa kowane mutum ko ƙungiya suna neman siffofin, daban-daban bukatar na kayayyakin da kuke fitarwa hakan zai ƙara maku adadin samun kuɗin shiga a kasuwanci ku.

3. Gano da aiwatar da ayyukan sadarwa iri-iri

Akwai hanyoyi daban-daban na yadda saƙon kamfani zai isa ga masu sauraro. Wannan zai taimaka masa ya daidaita kan waɗanni ayyuka zai shiga don a ci gaba da samar hanƴoƴi daban-daban don bunƙasa kasuwanci sa da ƙara adadin Kwastominmu ku.

4. Bayyana masu ruwa da tsaki.

Ma'aikata da sauran abokan aiki kamata mutane da suke aiki a Ƙarƙashin kasuwanci ka/ki su san irin gudunmawar da suke bayarwa ga kasuwancin da kuma irin sassan da suke da alhakin kulawa dashi hakan zai ƙarfafa masu Guywa.

Samun kyakkyawan tsari (biya masu buƙatar su da wadata su da kayan aiki) zai taimaka wajen tafiyar da nauyin da ke kansu Ya kamata abokan aikin ka/ki su san irin gudunmawar da suke bayarwa ga kasuwancin da akeyi da kuma irin sassan da suke da alhakin bayarwa da gudumuwar hakan zai ƙara ƙarfafa hanƴoƴin sadarwa na kasuwanci ku ko kamfanin ko Sana'o'in ku.

5. Saka masu ruwa da tsaki a harkar sadarwa.

Masu ruwa da tsaki na ɗaya daga cikin muhimman mutane da Kasuwanci ke buƙata . Samun wani tsari na musamman da aka tsara na sadarwa ga masu ruwa da tsaki zai bayyana irin ƙimar da Kasuwanci ku ke da ita wajen shigar da su.

6. A ƙara samun nasarar tsare-tsare da wuraren da ake buƙata na ƙarfafa hanƴoƴin yaƙi da irin waɗannan batutuwa. Za su iya samar da wata dabara ta musamman, da aka ƙayyade wacce aka tsara don tattara duk bayanan da take bukata don inganta shirin ku na bunƙasa kasuwancin ku ko Sana'o'i ku.

Ko wacce Sana'a ko kasuwanci kakeyi kana buƙatar tsarin Sadarwa don inganta sana'ar ka.

Kasuwar Baje-koli
Arzikin ku, a tafin hannun ku !!!

Menene Banbancin Strategic Alliance Da Partnership A Kasuwanci ? PARTNERSHIP:- haɗin gwiwa ne da mutane ke ƙullawa wajen...
20/03/2022

Menene Banbancin Strategic Alliance Da Partnership A Kasuwanci ?

PARTNERSHIP:- haɗin gwiwa ne da mutane ke ƙullawa wajen kasuwanci da zummar raba riba ko asara. Mafi yawa za ka ga mutane ne za su haɗu su samar da wata harka ta kasuwanci tare. Idan ta yi ruwa to rijiya. In kuma ba ta yi ba to masai.

STRATEGIC ALLIANCES:- Kasuwanci ne guda biyu ko sama da haka masu cin gashin kan su, za su ƙulla alaƙa don cigaban junan su kuma ba tare da wani daga cikin su ya sarayar da ƴancin sa ba. A irin wannan alaƙa, kwastomin waɗannan masu kasuwancin ɗin su ne su ka fi morewa wannan alaƙa domin don su aka yi ta.

Misali:- idan ka taɓa hawa jirgin da aka kawo ma ka abinci to ba kamfanin jirgin bane su ke abincin. Alaƙa suke ƙullawa da kamfanin abinci ko girke-girke. Ana ƙulla wannan alaƙa ne don su kamfanin jirgi su maida hankali wajen aikin su kar su raba hankalin su gida biyu. Idan su ka yi haka sai kamfanin da kwarewar su dama a abinci ta ke su yi su biya buƙatar fasinjojin da ke da buƙatar abinci.

Idan kun lura a cikin garin Kano za ku ga a wasu gidajen mai na Aliko za ku riƙa ganin an ware wani wuri ga masu kamfanin Rufaida Yoghurt. Wannan shi ne Strategic Alliance. Aliko Oil mai da gas da kalanzir su ke siyarwa amma saboda da samarawa da jama'a wurin da za su samu fura da nono da kaji sai s**a ƙulla alaƙa da Rufaida.

Idan ka je Tahir Guest Palace za ka ga Well Care a ciki. Well Care ba Hospitality Industry ne Kasuwancin su ba. Retail business su ke amma saboda masu hannu da shuni da ke mu'amala da Tahir sun ƙulla alaƙa don amfanar juna da cigaban kasuwancin su.

A kowani Kasuwanci ana buƙatar ƙulla alaƙa, don ƙarfafawa juna.

Kasuwar Baje-koli
Arzikin ku, a tafin hannun ku !!!

ABUBUWAN DA YA KAMATA KU SANI GAME DA KASUWAR BAJE-KOLI1- Kasuwar Baje-Koli: Za ta bada damar mallakar shaguna a dandali...
20/03/2022

ABUBUWAN DA YA KAMATA KU SANI GAME DA KASUWAR BAJE-KOLI

1- Kasuwar Baje-Koli: Za ta bada damar mallakar shaguna a dandalin yanar gizo, inda kowa zai zo ya tallata hajarsa kuma ya siyar kai-tsaye a kyauta.

2- Kasuwar Baje-koli; Za ta dinga koyar da darussa na kasuwanci da tattalin arziki na zamani, don samar da dabaru na zamani wajen bunƙasa ƙanana da matsakaitan sana'o'i.

3- Kasuwar Baje-koli; Za ta ba wa 'yan kasuwa masu shigo da kaya daga ƙasashen waje da kuma masu fitar wa zuwa ƙasahen ƙetare damar yin cinikayyar hajojinsu cikin sauki da rahusa.

4- Kasuwar Baje-kolin Kamfanin Life Trust Solutions Broadcasting International Limited ke da mallakinsa, kuma wani abun burgewar a na shi ne da harshen Hausa shi ne aka tsara manhajar domin saukakawa kwastominmu.

5- Kasuwar Baje-koli ta tanadar muku da kyakkyawan tsaro domin alkinta kayanku daga bata-garin yanar gizo.

Kasuwar Baje-koli
arzikin ku ce a tafin hannun ku !!!

Address

Kaduna South

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kasuwar Baje-Koli posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kasuwar Baje-Koli:

Share