Mahanga TV

Mahanga TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Mahanga TV, No 23 University Of Jos Consultancy Plaza Bauchi Road Jos, Kaduna.
(1)

05/03/2026

RAMADAN TAFSIR 13
Kenan Daga Masallacin SBB dake daura da KEYSTONE BANK T/Wada Makarfi.
Tare da;

Dr. Abdurrazak Kabir Makarfi, PhD

04/03/2026

Jadawalin Tafseer na watan Ramadan a Tashar mu ta Mahanga TV

27/02/2026

RAMADAN TAFSIR 08
Kenan Daga Masallacin SBB dake daura da KEYSTONE BANK T/Wada Makarfi.
Tare da;

Dr. Abdurrazak Kabir Makarfi, PhD

26/02/2026

RAMADAN TAFSIR 07
Kenan Daga Masallacin SBB dake daura da KEYSTONE BANK T/Wada Makarfi.
Tare da;

Dr. Abdurrazak Kabir Makarfi, PhD

23/02/2026

Alhamdulillah

22/02/2026

RAMADAN TAFSIR 04
Rana Ta Uku Kenan Daga Masallacin SBB dake daura da KEYSTONE BANK T/Wada Makarfi.
Tare da;
Dr. Abdurrazak Kabir Makarfi, PhD
Dauka
📹📹📹
Dalibai

21/01/2026

Allah ya gafartawa Shiekh Habibu Yahaya Kaura, Allah ya sa dan Aljannah ne. Ameen!😭🤲🏼

Inna lillahi Wa inna ilayhi Raji'oon😭😭😭😭Allah Ya Ƙarbi Rayuwar Malamin Mu, Kuma Baban Mu Sheik Habibu Yahaya Ƙaura,Yau L...
21/01/2026

Inna lillahi Wa inna ilayhi Raji'oon😭😭😭😭

Allah Ya Ƙarbi Rayuwar Malamin Mu, Kuma Baban Mu Sheik Habibu Yahaya Ƙaura,Yau Laraba 02-Sha'aban-1447H A Asibitin Nizamiyya dake Abuja.

Lokacin Jana’iza 4:30 a Helkwatar Jibwis Na Kasa Dake Utako Bega Abuja

Allah Ya Gafarta Masa Ya Kyautata Makwancinsa Yasa Jinya ta Zamo Kaffara.

Ameen

Kungiyar Tsofaffin Ɗaliban Na'ibi Academy Littahafizil Qur’ani Sun Karrama Shugaban JIBWIS na Ƙasa, Sheikh Imam Abdullah...
17/01/2026

Kungiyar Tsofaffin Ɗaliban Na'ibi Academy Littahafizil Qur’ani Sun Karrama Shugaban JIBWIS na Ƙasa, Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau

Kungiyar Tsofaffin Ɗaliban Makarantar Na'ibi Academy Littahafizil Qur’an sun shirya wani taro na musamman domin karrama Shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta Tarayyar Najeriya, Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau, bisa irin gagarumin gudunmawar da yake bayarwa wajen bunƙasa ilimi da kula da rayuwar ɗalibai.

Wannan karramawa ta biyo bayan ƙoƙari na musamman da Sheikh Bala Lau ke yi wajen tallafa wa ɗalibai, inda ya ɗauki nauyin karatunsu kyauta, tare da basu damar samun ilimin Alƙur’ani mai girma da na zamani cikin tsari da kulawa. Tsofaffin ɗaliban sun bayyana cewa wannan taimako ya taka muhimmiyar rawa wajen gina rayuwarsu, tare da zamar musu ginshiƙin nasara a fannoni daban-daban na rayuwa.

A cewar Kungiyar, abin da ya fi jan hankali shi ne yadda Sheikh Bala Lau ke gudanar da wannan aiki cikin ikhlasi da kishin addini, ba tare da neman yabo ko wata fa’ida ta duniya ba, sai dai burinsa na ilimantar da al’umma da gina ingantattun matasa masu tsoron Allah.

Shugabannin Kungiyar Tsofaffin Ɗaliban sun jaddada cewa irin wannan tallafi ya sa makarantar ta zama tushen haske da tarbiyya, inda ake haɗa ilimin addini da na zamani domin amfanin al’umma baki ɗaya. Sun kuma yi addu’a ga Sheikh Bala Lau da Allah Ya saka masa da alheri, Ya ƙara masa lafiya, tsawon rai da albarka a dukkan ayyukansa.

Hakika, wannan karramawa ta nuna cewa wanda ya zuba jari a ilimi, musamman ilimin Alƙur’ani, ya gina al’umma ne gaba ɗaya, kuma irin wannan aiki na Sheikh Imam Abdullahi Bala Lau abin koyi ne ga shugabanni da masu hannu da shuni a faɗin ƙasa.

Jibwis Nigeria

Ƙungiyar Izala zata yaye mahaddata Al'qurani sama da yara ɗari uku.Ƙungiyar Izala zata yaye mahaddata Al'qurani mai girm...
15/01/2026

Ƙungiyar Izala zata yaye mahaddata Al'qurani sama da yara ɗari uku.

Ƙungiyar Izala zata yaye mahaddata Al'qurani mai girma sama da yara ɗari uku a wannan sati tsakanin garin Lau, Jalingo a jahar Taraba da Jimetan jahar Adamawa a ranakun asabar lahadi da Litinin insha Allah.

Tun farko dai kamar yadda shafin Jibwis Nigeria ya ruwaito, Shahararriyar makarantar nan ta "TSANGAYAYAR SHAIKH ABDULLAHI BALA LAU FOR MEMORISATION OF HOLY QUR'AN" za ta yaye ɗalibai sama da ɗari da hamsin (150) tare da gabatar musu da walima a ɗakin taro na 'Taraba State Muslim Council' dake kusa da commissioners Qtrs, anguwar Nyamusala a Jalingon jahar Taraba a ranar Lahadi 28/Rajab/1447, 18/January/2026. Da misalin ƙarfe 10am na safe.

Kazalika Tawagar zata halarci garin Lau a ranar juma'a 16-01-2026 domin halartar bikin yaye mahaddata Al'qurani yara ɗari da biyar 105 a Makarantar Na'ibi A academy dake garin Lau da misalin ƙarfe tara na safe, washe gari asabar 17-01-2026 za'a halarci taron karɓan sabbin Dalibai a makarantar A.B. Na'ibi College of Nursing Science Lau, a kan titin mai kafi, unguwar Habu na biyu a cikin garin Lau dake Jahar Taraba

Akwai gagarumin wa'azin dare a ranar Alhamis 15/01/2026 a Masallacin Danfodiyo dake cikin garin Jalingo da misalin ƙarfe 8:00pm na dare insha Allah.

A ranar Litinin 19/01/2026, tawagar zata sauka a garin Jimeta domin gabatar yaye ɗalibai sama da saba'in (70) mahaddata Al'qurani mai girma a makarantar Na'ibi Academy dake garin Jimeta a jahar Adamawa, Sannan da gagarumin wa'azin dare da misalin ƙarfe 8:00pm na dare insha Allah.

Wasu daga cikin Malamai da zasu halarci wa'azin sun haɗa da:

-Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau
-Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo
-Sheikh Dr. Muhammad Kabir Haruna Gombe
-Sheikh Dr. Isma'il Kumo
-Sheikh Dr. Abdulƙadir Sale Kazaure
-Sheikh Dr. Ibrahim Idris Jos
-Sheikh Dr. Sadau Salihu Yola
-Sheikh Dr. Ibrahim Abdullahi R/lemo
-Sheikh Abdulbasir Isa Unguwar maikawo
-Sheikh Abubakar Mukhtar Yola
-Sheikh Gambo Kyari Maiduguri
-Sheikh Baba Bunu Maiduguri
-Alaramma Ahmad Suleiman Kano
-Alaramma Nasiru Salihu Gwandu
-Alaramma Mustapha Isa Jalingo

Manyan Baki:

-Shugaban agaji na ƙasa, Engr Mustapha Imam Sitti
-Shugaban JIBWIS na jahar Gombe, Engr Salisu Muhammad Gombe
-Shugaban JIBWIS na jahar Adamawa, Alhaji Sahabo Magaji

Sanarwa daga kwamitin Labaru ta kungiyar JIBWIS ta ƙasa.

Jibwis Nigeria

Jami’ar ta yi wannan kira a yayin wani taron yini daya da masana s**a shirya kan ina zamantakewar Hausawa ta dosa dangan...
15/07/2024

Jami’ar ta yi wannan kira a yayin wani taron yini daya da masana s**a shirya kan ina zamantakewar Hausawa ta dosa dangane da kallon fina-finan Hausa.

A cewar jami'ar kauracewa kallon finafinan, zai rage yaduwarsu da kuma yin amfani da miyagun darussan da ke cikinsu.

A ganinku wane tasiri finafinan suke da shi ga rayuwar al'umma?

Kuna ganin kauracewa kallonsu zai kawo wani sauyi tare da inganta rayuwar al'umma?

Rahma TV

Address

No 23 University Of Jos Consultancy Plaza Bauchi Road Jos
Kaduna

Telephone

+2347019103918

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mahanga TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Mahanga TV:

Share