26/05/2026
SANARWAN LOKACIN SALLAR IDI BABBA 1447/2026
Kungiyar Jibwis Kanam Nhqrs Jibwis Kanam Nhqr Jos karkashin jagorancin Ustaz Abudullahi Tukur (Jarman Jhar) tana farin cikin sanar da dukkan shugabannin rassa da sauran al'ummar musulmai na cikin garin Dengi da kewa cewa, za'a sai da Sallah (Kabarta sallah) da misalin karfe 08:30am (na safe) a gobe Laraba 10/12/1447H - 27/05/2026M.
Nan cikin garin Dengi, Idan ba'ayi ruwa ba za'a gabatar da sallah a babban masallacin Idi dake filin kwallon kafa na Kwalejin Gwamnati dake nan cikin garin Dengi (Government College, Dengi), idan kuma an tashi da ruwa za'a gabatar da sallah a babban masallacin Juma'a na I Jibwis Grand Masjid Dengi , wanda Hafiz, Imam Umar Adam Hussaini Dengi zai jagoranta.
Shugaban majalisar malamai na karamar hukuma Ustaz Abdullahi Hassan Tukur zai fara Nasiha da misalin karfe 07:30am In Sha Allah.
Duk wanda ya samu wannan sanarwa ya sanar da wanda bai sani ba domin a karfe 08:30am za'a sai da sallah babu kari Insha Allah.
N:B. Ana Umurtan dukkan Maluman da aka tura masallatan Idi na faɗin karamar hukuma wanda sunayen su ke rubuce acikin takardan dake nan, da suyi kira game da jin tsoron Allah, sannan suja hankalin mutane game da tuba zuwa ga Allah tare da yin addu'a ga kasa.
Sannan a karantar da jama'a muhimmancin Ibadah dake cikin wannan lokaci na sallah, muhimmancin lahiya da ka'idodin ta, sannan a faɗakar da mawadata muhimmancin taimakon mabukata.
Allah yasa ayi sallah lafiya, ya karbi dukkan Ibadarmu.
Abdulkarim Abubakar Ayuba Dengi
Jami'in Hulda da Jama'a
09 Dhul-Hijjah, 1447H
26 May, 2026M