23/12/2025
IMPORTANT ANNOUNCEMENT
ฦungiyar Women Online Vendors Association WOVA, ฦungiya ce ta mata masu kasuwanci a yanar gizo. Wannan kungiyar tana da members sama da 400 from all over Nigeria.
Mission ษin wannan ฦungiya shine "to educate women to do business better."
Wannan ya saka businesses din members ษin WOVA suke cigaba.
Sai dai a ฦดan kwanakin nan an samu wasu suna yiwa members na wannan ฦungiyar ungulu da kan zabo.
Sai su fito su nuna kansu a matsayin masu ilimin kasuwanci; idan s**a ga sun sami recognition, sai su damfari mutane.
A irin haka ne aka samu wani bawan Allah (name withheld for now) wanda yake bin members na wannan ฦungiya ya damfari wasu, wasu kuma ya janyo musu asara.
Don haka mata masu kasuwanci a yanar gizo ku kula:
โ Importation & Exportation suna da tsari da kuma hukumomin da suke kula da su. Kada ki yarda wani ya zo yace ki zo zai koya miki yanda zaki yi ki kai daddawarki ฦasar waje.
Idan kina son yin haka ki tafi ga hukumomi da kuma masana na ฦwarai.
โ Investors: Tabbas akwai mutanen da suke investing in other people's ideas, but ba da ka suke yi ba. Kada ki yarda wani mutum ya zo yace ki kawo kuษi zai haษaki da Investors; ba haka tsarin yake ba.
Idan ya samu Investors ษin ya riฦe ko shi bashi da wata idea ne?
โDuk registration ษin da k**e buฦata akwai masana masu yinsa da gaske kuma akwai hukumomin da suke yinsa; kada ki je ki zuba kudinki wajen ฦดan bogi ษarayin zaune.
A ฦarshe idan mutum yace zai baka riga ka dubi ta wuyansa.
Mu sani cewa akwai mutanen da zasu shisshige jikin wasu mutanen kirki masu ilimi; sai suyi amfani da reputation na wadancan su yi cuta.
Idan aka gansu tare da mutanen kirki sai a kyautata musu zato a amince da su; daga baya sai suyi zambo.
ฦungiya tana shirya taruka da bita lokaci zuwa lokaci. A duk lokacin da ฦungiya ta shirya bita ta kawo masana; to idan zaki ฦulla hulษa ta kuษi da wani da ฦungiya ta kawo ki tabbatar kin tuntuษi shugabancin ฦungiya.
Mata shine your eyes; wasu suna nan sana'arsu kawai shine su yi karatu su zo su nuna muku sun iya. Da zarar sun sami dama su kwashe muku kuษin da kuka ษauki lokaci kuna tarawa. Su kuma sana'arsu kenan.
Allah ya shiga tsakanin nagari da mugu.
Signed
Haj. Ayat Uba Adamu
Chairperson
WOVA
A saurari sanarwa ta gaba.....