Hausa Global Media

Hausa Global Media Distribution of educative contents for enlightenment and creating awareness.

𝐈𝐧𝐚 𝐁𝐚𝐒𝐰𝐚𝐭𝐚 π“πšπ€πž? πŸπŸ•Idan mun gamsu cewa kowa yana da wani abu da yake zuwa masa da sauΖ™i a rayuwarsa, ko da shi bai gano...
22/03/2026

𝐈𝐧𝐚 𝐁𝐚𝐒𝐰𝐚𝐭𝐚 π“πšπ€πž? πŸπŸ•

Idan mun gamsu cewa kowa yana da wani abu da yake zuwa masa da sauΖ™i a rayuwarsa, ko da shi bai gano hakan ba, to yana da kyau mu gane cewa, abu yana zuwa da sauΖ™i ne a dalili biyu. Dalilin farko da abu zai zo wa mutum da sauΖ™i shi ne baiwa, an haife shi da abun, kawai yana jiran a motsa baiwar ne. Dalili na biyu kuma shi ne horo.

Idan mutum ya samu horo a wannan fanni, bayan wasu shekaru zai samu Ζ™warewa ta ban mamaki har a Ι—auka ma iya baiwa ce kawai. Kenan dai ba kowanne abu da yake maka sauΖ™i ba ne yake cikin zubin halittarka ba, wasu abubuwan yau da gobe ce take horar da kai a kansu. Idan ka tashi a gidan wanzanci abu ne mai sauΖ™i ka samu gogewa a yin aski, har ya zama yana zuwa maka da sauΖ™i.

Wannan batu na kasa bambance abun da yake zuwa da sauΖ™i na baiwa, da wanda aka koya saboda mutum ya taso a cikin abun ya sa wasu ko da suna da baiwar ma ba sa iya gane cewa baiwa ce. Wasu kuwa kokonto hakan zai Ζ™ara musu, su dinga tunanin anya wannan baiwa ce ko don na taso a haka ne. Wasu hakan ma na iya jefa su cikin halin Ζ™in yarda da suna da wata baiwa, abun da s**a saba da shi kawai za su riΖ™e, daga sun gwada wani abu ya zo da tangarΙ—a sai su sa a ransu ba su da baiwa a wajen.

Ba koyaushe ba ne tsoron abu, ko gwadawa a karon farko a ji ba daΙ—i yake nuna babu baiwa a wajen. Misali, ban san cewa ina gane darasin lissafi ba sai da na shiga aji biyu (2) na Ζ™aramar sakandare saboda wata malama da muka samu. WataΖ™ila da ba don ta yi irin koyarwar da zan fahimta ba, da yanzu ina cikin masu gudun darasin
lissafi. Abun da ya fi wannan mamaki kuma, ita wannan malamar ta ba mu labarin yadda take Ζ™in lissafi, da yadda ba ta zama a ajin lissafi, amma kuma cikin ikon Allah a nan ta samu gurbin karatu a jami’a, haka ta daure ta yi, har ta zama haΙ—aΙ—Ι—iya.

Abun da ya kawo wannan batu shi ne, wani lokacin ba cikin sauΖ™i mutum yake iya yarda da abu a matsayin baiwarsa ba, saboda ko dai bai taso a kansa ba, ko kuma bai samu wanda zai koyar da shi a yadda zai fahimta ba. Wannan ya sa gane baiwa yake da alaΖ™a da yadda mutum yake koyo.

𝐀π₯𝐛𝐒𝐬𝐑𝐒𝐫: A halin yanzu π’π’Šπ’•π’•π’‚π’‡π’Šπ’ 𝑰𝒏𝒂 π‘©π’‚π’Šπ’˜π’‚π’•π’‚ π‘»π’‚π’Œπ’†? ya riga da ya kammala. In sha Allahu nan da wani lokaci za a bayyana inda za a samu softcopy Ι—in ga masu buΖ™atar saye. A saboda haka ba mamaki wannan ya zama rubutu na Ζ™arshe da zan kawo daga cikin wannan littafin. Allah ya taimake mu.

π˜Όπ™π™’π™–π™™ π™Žπ™–π™£π™ž
#𝙃𝙖π™ͺπ™¨π™–π™‚π™‘π™€π™—π™–π™‘π™ˆπ™šπ™™π™žπ™–
22/3/2026

21/03/2026

Big shout out to my newest top fans! Maryam Rabiu Yusuf, Abdulmutallab Zakariyya, Ibrahim Shu'aibu

Abota a dandalin sada zumunta  21/3/2026
21/03/2026

Abota a dandalin sada zumunta


21/3/2026

Dukkaninmu da ke Hausa Global Media muna yi muku barka da sallah, Allah ya karΙ“a mana ya kuma maimaita mana. πŸŒ™   πŸŒ™
21/03/2026

Dukkaninmu da ke Hausa Global Media muna yi muku barka da sallah, Allah ya karΙ“a mana ya kuma maimaita mana.

πŸŒ™

πŸŒ™

21/03/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Tukur Bello Adamu, Maryam Rabiu Yusuf, Umar Lyman, Ω…Ψ¨Ψ΄Ψ± Ψ§Ω„Ψ―ΩˆΩŠΨ΄ΩŠ

30-09-1447
19/03/2026

30-09-1447



  18/3/2026
18/03/2026


18/3/2026

29-09-1447
18/03/2026

29-09-1447



28-09-1447
17/03/2026

28-09-1447



27-09-1447
16/03/2026

27-09-1447



26-09-1447
15/03/2026

26-09-1447



Address

Hotoro Rakad
Kano
700223

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Global Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa Global Media:

Share