Kadial News

Kadial News Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Kadial News, Kano.

Dr. Kabiru Getso Yayi Ta'aziyyar Rasuwar Alhaji Adamu Getso (Galadiman Getso) Tsohon Kwamishinan Ma'aikatun Lafiya da Mu...
07/06/2026

Dr. Kabiru Getso Yayi Ta'aziyyar Rasuwar Alhaji Adamu Getso (Galadiman Getso)

Tsohon Kwamishinan Ma'aikatun Lafiya da Muhalli na Jihar Kano, kuma Memba a Kwamitin Gudanarwa na Jami'ar Sufuri ta Tarayya da ke Daura, Hon. Dr. Kabiru Ibrahim Getso, ya bayyana matuƙar alhini da jimami bisa rasuwar Alhaji Adamu Ibrahim Getso, tsohon Manajan Darakta na Radio Kano da ARTV.

A cikin wata sanarwa da Mai Taimaka Masa na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama'a, Aliyu Abdul Garo, ya fitar, Dr. Getso ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban rashi ga al'ummar Getso, Jihar Kano baki ɗaya, da kuma fannin yaɗa labarai.

Ya ce labarin rasuwar Alhaji Adamu Ibrahim Getso ya girgiza shi matuƙa, tare da haifar da babban gibi da zai yi matuƙar wahalar cikewa, la'akari da irin gudunmawar da marigayin ya bayar wajen ci gaban al'umma da hidimomin jama'a a tsawon rayuwarsa.

Dr. Getso ya bayyana marigayin a matsayin jagora nagari, mai ba da shawara, gogaggen mai gudanarwa, kuma uba ga al'ummar Getso, wanda hikimarsa, nagartarsa, da jajircewarsa wajen cigaban al'umma s**a sanya ya samu girmamawa da karramawa daga jama'a daban-daban.

Ya ce, "Na yi matuƙar alhini da jin rasuwar Alhaji Adamu Ibrahim Getso. Wannan babban rashi ne ga al'ummarmu da ma jihar Kano baki ɗaya. Marigayin ba kawai ginshiƙi ne ga iyalansa ba, ya kasance uba, jagora, kuma abin koyi ga al'ummar Getso baki ɗaya. Gudunmawar da ya bayar a fannin yaɗa labarai, cigaban al'umma da gina ɗan Adam za su ci gaba da kasancewa abin tunawa har abada."

A madadinsa, iyalansa, magoya baya da masoyansa, Dr. Getso ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, Dagacin Getso Alhaji Bello Ibrahim (San Getso), al'ummar garin Getso, abokai da masu ruwa da tsaki, tare da daukacin al'ummar Jihar Kano bisa wannan babban rashi.

Ya kuma bayyana cewa marigayi Alhaji Adamu Ibrahim Getso ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al'umma hidima, inganta walwalar jama'a, da bunƙasa harkokin yaɗa labarai, inda ya bar kyakkyawan tarihi da za a ci gaba da alfahari da shi tsawon lokaci.

Dr. Getso ya ƙara da cewa, "Babu shakka rasuwar Alhaji Adamu Ibrahim Getso babban rashi ne ga al'ummar Getso da karamar hukumar Gwarzo baki ɗaya. Tarihin rayuwarsa na gaskiya, riƙon amana, shugabanci nagari da hidimtawa jama'a zai ci gaba da zama abin koyi ga masu zuwa bayansa."

Daga ƙarshe, ya yi addu'ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin, Ya yafe masa kura-kuransa, Ya sanya shi a Aljannatul Firdaus, tare da bai wa iyalansa, 'yan'uwansa da daukacin masoyansa haƙurin jure wannan babban rashi.

Aliyu Abdul Garo
07 June 2026
Sunday.

SANARWAR MANEMA LABARAIDR. GETSO YA TAYA MUSULMAI MURNAR BABBAR SALLAH Tsohon Kwamishinan Ma’aikatun Lafiya da Muhalli n...
28/05/2026

SANARWAR MANEMA LABARAI

DR. GETSO YA TAYA MUSULMAI MURNAR BABBAR SALLAH

Tsohon Kwamishinan Ma’aikatun Lafiya da Muhalli na Jihar Kano, kuma Mamba a Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Sufuri ta Tarayya da ke Daura, Hon. Dr. Kabiru Ibrahim Getso, ya taya al’ummar Musulmin Najeriya da ma duniya baki ɗaya murnar bikin Babbar Sallah.

A cikin wata sanarwa da Mai Taimaka Masa na Musamman kan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a, Aliyu Abdul Garo, ya fitar, Dr. Getso ya bayyana Babbar Sallah a matsayin babban tunatarwa kan imani, sadaukarwa, biyayya da tausayi. Ya buƙaci Musulmai da su yi koyi da darussan Annabi Ibrahim (AS) ta hanyar ƙara kusanci ga Allah tare da tallafa wa junansu, musamman marasa galihu a cikin al’umma.

Dr. Getso ya kuma aike da saƙonnin fatan alheri ga manyan shugabanni ciki har da tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, inda ya yi masa addu’ar samun ƙoshin lafiya, da kwarin guywa wajen ci gaba da hidimtawa al’umma.

Haka zalika, ya taya Gwamnan Jihar Kano Alh. Abba Kabir Yusuf, da Mataimakin Gwamnan Jihar, Alh. Murtala Sule Garo, tare da sauran shugabannin siyasa na jihar murnar wannan biki. Tare da yabawa Gwamnan bisa jajircewarsa wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da ke inganta zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba mai ɗorewa a jihar.

Sanarwar ta kuma yaba da muhimmiyar rawar da sarakunan gargajiya, malamai da shugabannin addinai ke takawa wajen inganta kyawawan ɗabi’u, zaman lafiya da haɗin kai tsakanin al’umma.

Dr. Getso ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci na Sallah wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa, rungumar juna da kauce wa duk wani nau’i na rarrabuwar kawuna, tashin hankali da ƙiyayya. Ya jaddada cewa zaman lafiya, mutunta juna da haɗin kai su ne ginshiƙan samun ci gaba mai dorewa da bunƙasa ƙasa.

A ƙarshe, ya yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya karɓi ibadu, sadaukarwa da ayyukan alheri na al’ummar Musulmi, Ya gafarta kura-kurai, Ya Albarkaci jihar Kano, Najeriya da daukacin al’ummar Musulmi na duniya da zaman lafiya, wadata da kwanciyar hankali mai ɗorewa.

Aliyu Abdul Garo
28 ga Mayu, 2026
Alhamis.

Muna zargin Baffa Babba Ɗan'agundu da yiwa Jam'iyyar APC zagon ƙasa.Babu ko shakka maganganun da Baffa Babba yakeyi a wa...
21/05/2026

Muna zargin Baffa Babba Ɗan'agundu da yiwa Jam'iyyar APC zagon ƙasa.

Babu ko shakka maganganun da Baffa Babba yakeyi a wannan gaɓar zagon ƙasa ne da neman rarraba kawunan ƴaƴan jam'iyyar APCn Jihar Kano musamman Shiyyar Kano ta Arewa wacce itace GOLDEN ZONE a gurin dukkanin wani ɗan tsohuwar jam'iyyar APC, Shiyyar da ita kaɗai ce Jam'iyyar APC taci Sanata da Ƴan Majalissu ta kawowa shugaban ƙasa kuri'a tare da ɗan takarar gwamna na wancan lokacin, duk wani me kishin jam'iyyar APC da son tayi nasara a jihar Kano bazai rinƙa yin kalamai na tunzuri da rarraba kawunan ƴaƴan jam'iyyar ta APC ba, musamman ya rinƙa ƙara rura wutar fitina tsakanin Sanata Barau da ATM Gwarzo wanda sun riga sun haɗe zasu yiwa APC aiki tun daga sama har ƙasa, a wannan gaɓar da tafi kowacce gaɓa haɗari, gaɓar da ake taka tsantsan da gudun faɗawa cikin rarrabuwar kawunan ƴaƴan jam'iyya a gaɓar shi Baffa Babba Ɗan'agundu zai fito yana iƙirarin babu sulhu a siyasar wani yanki daba nasa ba.

Duk wani ɗan Jam'iyyar APC dama wanda ba ɗan Jam'iyyar ba idan ka tambaye shi wanne zone ne ko kokwanto basayi zone ɗin Jam'iyyar APC ne kuma ko tantama ba'ayi akan Nasarar jam'iyyar APC a yankin da ɗan Jam'iyyar APC dama wanda ba ɗan Jam'iyyar ba zai ce maka Shiyyar Kano ta Arewa, Shiyyar da kowa yake da tabbaci a kanta, Shiyyar da a 2023 ita kaɗai ce Jam'iyyar APC tai Nasara amma Baffa Babba ya fito yake ƙoƙarin raba kawunan Mutane a Shiyyar, yankin da ba nasa ba.

Baffa Babba Ɗan'agundu Maimakon Kalaman tunzuri da katsalandan a cikin siyasar wani yanki daba naka ba zaifi kyau ka koma ka gyara siyasar yankin ka, tun daga matakin akwatu zuwa mazaɓa har zuwa ƙaramar hukumar ka, ina ganin wannan aiki shine yafi maka ba fitowa kana rura wuta a wani yanki daba naka ba, Jam'iyyar APC a Shiyyar Kano ta Arewa zaune take lafiya kuma muna da tabbacin ruɓanya ƙoƙarin ƴaƴan jam'iyyar ta APC akan samun nasarar cin zaɓe a 2027 tun daga sama har ƙasa.

Muna kira ga uwar Jam'iyyar APC ta Jihar Kano da mai girma Gwamna da dukkanin jagororin Jam'iyyar APC na jiha dama ƙasa dasu tsawatarwa da Baffa Babba Ɗan'agundu kan zagon ƙasa da kalaman tunzuri da yakeyi kan siyasar Shiyyar Kano ta Arewa zone ɗin da duk ɗan Jam'iyyar APC yake kiran sa da (GOLDEN ZONE). Sannan su bashi assignment da yakoma yankinsa musamman ma akwatinsa da ƙaramar hukumar sa kada wannan lokacin ma yabamu kunya ya kasa ciwo mana zaɓen su.

Nasarar APC itace a gaban mu.

Hon. Abdullahi Abubakar
Ɗan kishin jam'iyyar APC

HOTUNA: Yadda aka yi jana'izar Birgediya-Janar Braimah da sauran sojojin da ƴan Boko Haram su ka kashe a Borno
15/04/2026

HOTUNA: Yadda aka yi jana'izar Birgediya-Janar Braimah da sauran sojojin da ƴan Boko Haram su ka kashe a Borno

Gwamnatin Tarayya ta gyara tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon ministan shari'a Abubakar Malami, inda ta cire zargin ɗauk...
15/04/2026

Gwamnatin Tarayya ta gyara tuhume-tuhumen da ake yi wa tsohon ministan shari'a Abubakar Malami, inda ta cire zargin ɗaukar nauyin ta’addanci, ta maye gurbin sa da zargin mallakar mak**ai ba bisa ka’ida ba.

A yayin zaman kotun, Malami da ɗansa sun musanta sabon zargin, yayin da alkalin, Joyce Abdulmalik, ta ba su damar ci gaba da zama a beli.

An ɗage shari’ar zuwa ranar 26 ga Mayu da 15 ga Yuni domin ci gaba da sauraro.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ayyana yaƙin “ba sani ba sabo” kan cin hanci da rashawa, inda ta gargaɗi jami’anta ...
15/04/2026

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta ayyana yaƙin “ba sani ba sabo” kan cin hanci da rashawa, inda ta gargaɗi jami’anta da ke kan hanyoyi cewa duk wanda aka k**a da laifi zai yaba wa aya zaƙinta.

Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa ambaliya za ta shafi jihohi da dama a Najeriya, ciki har da Bayelsa, Delta, Adamaw...
15/04/2026

Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa ambaliya za ta shafi jihohi da dama a Najeriya, ciki har da Bayelsa, Delta, Adamawa da Kebbi, a shekarar 2026.

Rahoton ya nuna cewa dubban al’ummomi a jihohi 33 da Abuja na cikin haɗarin ambaliya mai tsanani, yayin da wasu da dama za su fuskanci matsakaici ko ƙananan haɗari.

Haka kuma, an yi hasashen ambaliya a manyan birane k**ar Kano, Lagos da Abuja sak**akon ruwan sama mai yawa da matsalolin magudanan ruwa, tare da yiwuwar ambaliyar teku a jihohin bakin ruwa.

Gwamnati ta bukaci jihohi, ƙananan hukumomi da al’umma su fara shiri tun yanzu domin rage illar ambaliyar.

06/04/2026
Hukumomin rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) sun tabbatar da mutuwar babban jami’in leƙen asirin su, Majid Khademi, b...
06/04/2026

Hukumomin rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) sun tabbatar da mutuwar babban jami’in leƙen asirin su, Majid Khademi, bayan wani hari ta sama da aka kai masa a safiyar yau.

A cewar wata sanarwa da aka wallafa ta kafar labarai ta Tasnim, Khademi ya rasu ne sak**akon harin da ya afka masa, duk da cewa ba a bayyana cikakken bayani kan wurin da lamarin ya faru ba.

Rahotanni sun nuna cewa marigayin ya rike muhimman muk**ai guda biyu a cikin IRGC, inda ya kasance shugaban sashen kare bayanan sirri (Intelligence Protection Organization) da kuma jagoran sashen leƙen asiri (Intelligence Organization) na rundunar.

Har zuwa yanzu dai babu wata sanarwa daga Isra'ila dangane da zargin hannu a harin, lamarin da ke ƙara jefa tambayoyi kan wanda ke da alhakin kai wannan farmaki.

Mutuwar Khademi na zuwa ne a wani lokaci da ake ci gaba da fuskantar tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, inda hare-hare da martani ke ci gaba da ƙara k**ari tsakanin ƙasashe Amurka-Israila da Iran.

Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari a ƙauyen Ariko da ke ƙaramar hukumar Kachia a Jihar Kaduna, inda s**a kai farmaki kan maj...
05/04/2026

Wasu ‘yan ta’adda sun kai hari a ƙauyen Ariko da ke ƙaramar hukumar Kachia a Jihar Kaduna, inda s**a kai farmaki kan majami’u biyu a yayin bikin Easter, s**a kashe aƙalla mutane bakwai tare da sace wasu da dama.

Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne da safiyar ranar Lahadi, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da tashin hankali.

Dan majalisar yankin Awon Ward, Mark Bawa, ya tabbatar da faruwar lamarin ta wayar tarho, inda ya ce majami’un da abin ya shafa sun haɗa da First ECWA Church da kuma St. Augustine Catholic Church da ke Ariko.

Ya ce har yanzu ana tattara cikakken bayani kan adadin waɗanda s**a mutu, domin wasu rahotanni na cewa mutum bakwai ne s**a rasu, yayin da wasu ke cewa sun kai takwas.

A lokacin da aka tuntubi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, ya ce za su fitar da cikakken bayani kan lamarin nan gaba.

Address

Kano

Telephone

+2348062237474

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kadial News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kadial News:

Share