21/09/2026
🟢 2027: ITA MA DARIKAR QADIRIYYA TA BAYYANA GOYON BAYANTA GA TINUBU
Jagoran darikar Qadiriyya a Afirka, Sheikh Qaribullah Sheikh Nasiru Kabara, ya bayyana goyon bayan darikar ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
Sheikh Qaribullah ya bayyana hakan ne ranar Lahadi, 20 ga Satumba 2026, lokacin da ya karɓi tawagar yaƙin neman zaɓen Tinubu, ƙarƙashin jagorancin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC, Sanata Abdul’aziz Yari.
Malamin ya ce naɗin Yari ya ƙara ƙarfafa alaƙar da ke tsakanin darikar Qadiriyya da tawagar yaƙin neman zaɓen, yana mai cewa Sanatan ya shafe sama da shekaru 20 yana da kusanci da darikar.
«“Fiye da shekaru 20 muna tare da Abdul’aziz Yari, kuma ya kasance yana nuna goyon bayansa ga wannan gida. Yana daga cikinmu, saboda haka duk abin da ya zo da shi, ba mu da wani zaɓi face mu goyi bayansa,” in ji Sheikh Qaribullah.»
Sheikh Qaribullah ya ce baya ga goyon bayan Tinubu domin ya sake komawa kan kujerar shugaban ƙasa, darikar ta yi imanin cewa shugaban yana da “kyakkyawar manufa” ga Najeriya.
Ya kuma bayyana cewa Qadiriyya za ta fara gudanar da addu’o’i tare da mabiyanta, inda za a mayar da hankali kan zaman lafiya, farfaɗowar tattalin arziki, samar da ayyukan yi ga matasa da kuma kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro.
A nasa jawabin, Sanata Abdul’aziz Yari, wanda ya samu rakiyar tsohon Gwamnan Kano kuma tsohon Shugaban APC na Ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, da James Faleke, Sanata Ali Modu Sheriff, Aminu Masari, Adamu Aleiro da sauran ’yan tawaga, ya ce sun fara ganawa da malaman addini ne saboda irin mutuncin da suke da shi a cikin al’umma.
Me kuke ganin wannan goyon baya na Qadiriyya zai iya haifarwa a siyasar 2027?
#2027
Ku Danna Follow Domin Samun Sabbin Labarai