17/08/2026
NA TAUSAYAWA MUSA MAISANA: WATAKILA BAI FAHIMCI INDA YA SHIGO BA 😔
Abin da ya faru da jarumi Musa Maisana a Katsina abin tausayi ne, kuma gaskiya akwai darasin da ya k**ata a koya daga lamarin.
Ba wai rainin wayo ba ne ga Maisana, amma a ganina bai fahimci irin yanayin da yake shiga ba. Katsinawa da al’ummar yankin sun dade suna bayyana matsalolinsu da irin abubuwan da suke fuskanta, don haka zuwa tsaye a tsakiyar jama’a domin isar da saƙon siyasa da ba su amince da shi ba, musamman a irin wannan yanayi, abu ne da zai iya haifar da tashin hankali.
Wallahi idan ba ka san yanayin gari ba, ba ka tashi ka hau ganuwar garinsu kana musu abin da zai fusata su ba. 😔
Musa Maisana jarumi ne, kuma ya k**ata a kare rayuwarsa k**ar yadda ake kare rayuwar kowa. Amma shi ma wannan lamari ya zama darasi gare shi da sauran masu shiga harkar wayar da kai:
Ba kowane wuri ne ya dace a je da irin saƙo guda ba.
Allah Ya kiyaye gaba, Ya ba kowa hikimar sanin lokacin magana, lokacin yin shiru, da kuma lokacin janye wa domin kare kai.
Katsinawa ma Allah Ya kyauta—fushi bai k**ata yakai ga bugu ba 🤲