16/04/2026
Noman Inibi (Grapes 🍇)
Idan har ka shiryawa wanga noma, kana iya samun miliyoyin kudi kana daga kwance.
Manoma inibi suna samun kudi, wanda ba kowa yasan irin alkairin dake cikin wannan noma ba, sai idan masu yinta sun hasakwa mutum.
Akwai wani manomin inibi da yake bada labari, yana da gonar inibi wadda girmanta ya kai hactare guda, a cikin wannan gona yana da inibi kimanin tushe 2,400. Suna diban shi (harvesting) sau 2 a shekara. Akalla kowacce tushe guda daya tana bayar da amfani wanda yawanshi baya gaza kilo 6-8 (kg), wasu yana haura haka.
A tushe 2,400 da yake dasu yana samun kilo 14,000 - 16,000 (kg), a tone zai k**a 14-16 tones, kenan, a kowanne diba (harvest) da akayi. Kuma a shekaran ana diba sau biyu.
Yana siyar da kowanne kilo akan kudi naira 5000 - 6000. Idan ka hada lissafin gaba daya zai baka naira miliyan 85 - 90(M), duk bayan wata 6.
Abun da yake samu ashekara baya gaza miliyan 160 - 180(M).
Cigaban da aka samu a wannan fanni na Inibi, yanzu ana samun wayanda idan an shuka su, an basu kulawar data dace sosai da sosai, suna fara yin ya'ya a shekara daya.
Sannan ita wannan shuka ta inibi indai ana kula da ita, ta kan rayu har tsahon shekara 50 ana amfanuwa daga gareta.
Sannan ita wannan kasuwar ta inibi, kasuwa ce da masu siye koda yaushe suna nan, da zarar sun san kana dashi, zasu biyoka har inda kake, su siya daga gareka.
A yanzu haka a Nigeria kaso 60% na abun da muke bukata ana kawo mana shine daga kasar Morocco da South Africa, bama iya samar da abun da ake bukata din.
Wannan shine dalilin dayasa, kullun kasuwar cikin bukata take, a yanzu haka akwai kungiya ta manoma Inibi da suke da cibiya a jahar kaduna, wanda indai ka zama dan wannan kungiya, su da kansu zasu hadaka da masu siyan kayan naka.
A jiya mun samu kai musu ziyara wannan gonar tasu da take karamar hukumar kudan, Kaduna State, mun samu amfanuwa daga ilimi sosai, abun sai wanda ya gani Alhamdulillahi.
Amfanin irin wannan investment din idan mutum yayi shi, to fa ba kai k