28/08/2023
Da sanyin safiyar ranar Litinin 20 ga watan Maris na shekarar 2023, baturen zaΙe na jihar Kano, Farfesa Ahmad Doko Ibrahim, ya bada sanarwar sakamakon zaΙen gwamnan jihar, bayan tattara kuri'un kananan hukumomi 44 da ke jihar, cikin zaΙen da ya gudana Ranar Asabar 18 ga watan Maris 2023.
Injiniya Abba Kabir Yusuf, na jam'iyyar NNPP shi ne ya cika dukkan Ζa'idojin samun nasara a zaΙen, kuma aka bayyana shi a matsayin wanda yayi nasara, harma hukumar zaΙe mai zaman kanta ta Ζasa INEC, ta bashi shaidar samun nasara.
A ranar 29 ga watan Mayu ne aka rantsar da Abba a matsayin zaΙaΙΙen gwamnan Kano, watanni uku kenan da s**a gabata, wanda kuma tuni ya fara aiwatar da ayyukan da yayi alkawari a lokacin yaΖin neman zaΙe, bayan kafa majalisar zartarwar gwamnatinsa.
Ya kuka kalli kamun ludayin gudanarwar gwamnatin Abba?
28/8/2023