Ka De Ja Dj

Ka De Ja Dj 1994
Kano state

Idan ka yi wa rayuwarka tsari, ba ka buƙatar gaggawa, gaggawa aikin mara tsari ce. Ka yi aiki tuƙuru wajen neman abin da...
22/04/2025

Idan ka yi wa rayuwarka tsari, ba ka buƙatar gaggawa, gaggawa aikin mara tsari ce.

Ka yi aiki tuƙuru wajen neman abin da zai amfane ka a duniya da lahira.

Duk wani abu mai kyau sai an wahala ake samu, idan ka ce shortcut za ka bi, to biyu babu za ka yi.

A shekarar 1880 sarauniyar kasar Thailand ta rasu ta hanyar nutsewa a cikin ruwa duk da hadimanta da bayinta suna ganint...
22/04/2025

A shekarar 1880 sarauniyar kasar Thailand ta rasu ta hanyar nutsewa a cikin ruwa duk da hadimanta da bayinta suna ganinta ba tare da sun yi kokarin ceto ta ba.

Dalilinsu kuwa shine dokar masarautar ta harmatawa bayin sarauniyar taba jikinta.

Imam Maleek Auwal Warure

BA, A SAMUN  DUNIYA DA SANYIN JIKI, SAI DA ƘOƘARI.Ba ƙarfin zuciyar Hi**er ba ce,Ko dabarar Stalin,Ko kwaikwayon wayon C...
21/04/2025

BA, A SAMUN DUNIYA DA SANYIN JIKI, SAI DA ƘOƘARI.

Ba ƙarfin zuciyar Hi**er ba ce,
Ko dabarar Stalin,
Ko kwaikwayon wayon Churchill,
Sai dai wutar da ke ƙirjin matashi, Mai son Jajircewa akan abinda yake so.

Wanda ya ƙi dogaro da tsammani, Yayi Fafutuka da Gumin dake Fita a jikinsa ,
Ya tashi da safe da sunan:
"Zan nemi na kaina!"

Ba don ya ga hanya a buɗe ba,
Amma don yasan cewa duk Wani Bango Za'a iya Keta Hanya ta jikinsa a wuce duk ƙarfinsa.

Kar ka raina ƙanƙantar sana'a,
Kar ka ɗauki dinki ko aski a matsayin ƙasƙanci,
Kar ka yi tunanin shan ruwa da tsintar kwalabe
Ya fi mutunci da za a samu a Libya ko Aljeriya.

Sana'ar da ka raina anan ka kasa jajircewa akanta ko a can ƙasashen da kake hange ko darajar Wanda s**a kai Rabin su ba zaka samu ba.

Ba kowanne ke da Sa'a ba idan wani yayi rawa ya samu kuɗi wani na jakki zai ci.

Duk mai hakuri yana girbi.
Kamar yadda dundu take karyewa,
A hankali kuma take zama kasko,
Haka sana’a take — a hankali ake gina ta.

In ka dage da gaskiya,
Ka rungumi aiki — ko ɗinki ne, ko suya, ko gyaran waya —
Wallahi zakaci nasara fiye da wanda ya haura hamadar Sahara,
Ya bar gida da fata, amma ya dawo da baƙin ciki.

Fita daga ƙasa ba laifi ba ne,
Amma idan ta zama dole —
To ka sani: akwai wahala da azaba,
Rayuwa bata da tausayi,
Kuma ba duk wanda ya fita ke dawowa da dariya.

Amma kai matashi!
Ka tsaya — ka jajirce — ka nemi na halal,
Duniya ba ta jin kuka,
Amma tana lale marhabin da ƙoƙari.

Ka zama dutse a ruwa,
Ka zama murya a shiru,
Ka zama gwarzo a cikin rayuwa,
Domin duk mai hakuri,
Allah baya barinsa a baya.

SHIN HAKA MUKE KOH MUN CANZA?😥Shehu Aliyul Harazimi Hausawa RTA yace:"Idan Mutum Yazo Kuka Gaisa Kayi Shiru,Idan Yana Da...
20/04/2025

SHIN HAKA MUKE KOH MUN CANZA?😥

Shehu Aliyul Harazimi Hausawa RTA yace:

"Idan Mutum Yazo Kuka Gaisa Kayi Shiru,
Idan Yana Da Buƙata Yafada,

Idan Yakawo Maka Zancen Wani Kace Baka Sani Ba,
Idan Yakawo Maka Hirar Duniya Kace Baka Sani Ba,

Idan Yakawo Maka Sha'anin Zancen Yan Duniya Kace Baka Sani Ba,
Idan Kayi Haka Kahuta, Idan Kayi Shiru Katsira....

ALLAH Ya Jaddada Maka Rahama Albarkan Manzon ALLAH Sallallahu Alaihi Wasallam 🤲💖🤲💖🤲

FT: Leicester City 0-1 Liverpool FC. BREAKING: Leicester City RELEGATED Daga Premier League!
20/04/2025

FT: Leicester City 0-1 Liverpool FC.

BREAKING: Leicester City RELEGATED Daga Premier League!

Wannan haka yake
20/04/2025

Wannan haka yake

Wana gri ne s**a fi iya soya nmaa?
20/04/2025

Wana gri ne s**a fi iya soya nmaa?

Wanne Kallo kuke yiwa mace da ke sanya wannan ba tare da kasancewarsa  al'adarsu ba?
20/04/2025

Wanne Kallo kuke yiwa mace da ke sanya wannan ba tare da kasancewarsa al'adarsu ba?

WATARANA ALLAH YA TAMBAYI MALA'IKAN MUTUWA😭Shin baka taɓa yin kuka ba a yayin da kake karɓar ran Ɗan Adam?Sai mala'ikan ...
18/02/2025

WATARANA ALLAH YA TAMBAYI MALA'IKAN MUTUWA😭

Shin baka taɓa yin kuka ba a yayin da kake karɓar ran Ɗan Adam?

Sai mala'ikan yace:

Nayi kuka sau ɗaya, nayi dariya sau ɗaya sannan na firgita sau ɗaya 😢

Sai Allah Yace masa:

Me ya baka dariya ne?

Sai yace: abunda ya bani dariya shine, naje karɓar ran wani mutum sai na iske shi yana cewa mai yi masa takalmi: ka kyautata ƙirar takalman nan, ka ƙira su yadda zan saka su har tsawon shekaru biyar 😢

Sai nayi dariya na ɗauki ransa tun bai saka su ba koh sau ɗaya 😭

Sai Allah Yace masa: toh me yasa ka kuka ya kai mala'ikan mutuwa?

Sai yace:

Abunda ya sakani kuka shine: watarana naje karɓar rayuwar wata baiwar Allah wacce take ita kaɗai a cikin wani babban jeji, da naje sai na iske ta tana haihuwa sai na jira har ta haihu sannan na ɗebe ran nata 😭
Sai kukan jaririn da na bari a jejin shi kaɗai baya da wanda zai kula shi ya sakani kuka 😭😭😭

Sai Allah Yace masa: toh me ya firgitar da kai?

Sai yace: abunda ya firgitar dani shine:

Watarana naje karɓar rayuwar wani malami daga cikin bayin ka sai na iske haske yana fita daga ƙofar ɗakinsa.

Duk lokacin da na kara kusantar ɗakin sa sai hasken nasa ya haska ya mayar dani, sai abun ya firgita Ni 😭

Sai Allah Yace masa: Ya kai mala'ikan mutuwa shin kasan waye wannan mutumen da hasken sa ya firgitar dakai, kasan waye Shi???

Sai yace: A'a!

Sai Allah Yace masa: Wannan mutumen da hasken sa ya firgitar dakai shine Ɗan yaron matar nan da ka ɗauke ranta a jeji ka bar shi shi kaɗai bbu mai kula dashi ✍️

Na kula dashi, na bashi kariya har ya zamo abunda ya firgita ✍️

LA ILAHA ILLALLAH 😭😭😭

TABBAS SHA'ANIN UBANGIJI DABAN YAKE 😭

YA UBANGIJI KAYI MANA SAUQIN FITAR RAI 😭😭🙏

YA ALLAH KA KULA DAMU KUMA KA SHIGA LAMURAN MU KAMAR YADDA KA SHIGA LAMURAN WANNAN JINJIRIN 🙏😭😭

Idan labarin yayi tasiri a gareka kaima kayi sharing saboda 'yan uwa su amfana 🙏

17/02/2025

Address

Kano State Nasarawa Local Government
Kano

Telephone

+2347026901936

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ka De Ja Dj posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Ka De Ja Dj:

Share