21/12/2025
MATASA A NEMI SANA’A
Sana’a ita ce ginshiƙin rayuwar ɗan Adam. Ta hanyar sana’a ne mutum ke dogaro da kansa, yana kauce wa zaman banza da dogaro ga wasu.
Sana’o’in Annabawa a matsayin abin koyi
Allah Maɗaukakin Sarki ya zaɓi Annabawa masu daraja, amma duk da hakan, sun kasance masu sana’a da aiki:
• Annabi Adam (AS) ya yi noma da kiwo, domin samar da abinci.
• Annabi Musa (AS) ya yi kiwo, yana hidima da dogaro da kansa.
• Annabi Ibrahim (AS) ya yi aikin gini, inda ya gina Ka’abah tare da ɗansa Isma’il.
• Annabi Dauda (AS) ya yi ƙira, yana ƙera kayan yaƙi da hannunsa.
• Annabi Nuhu (AS) ya yi kafinta, ya ƙera jirgin ruwa bisa umarnin Allah.
• Annabi Muhammadu (SAW) ya yi kiwo da kasuwanci, yana neman halal tun kafin a aiko shi Manzo.
Akwai sana’o’i da dama da matasa za su iya koya ko yi gwargwadon ƙarfinsu da sha’awarsu, daga cikinsu akwai:
Sana’o’in gargajiya
• Noma
• Kiwo
• Farauta
• Kamun kifi
• Saƙa
• Sassaka
• Suss**a
• Wanzanci
• Rini
• Fawa
• Tela
• Kafinta
• Ƙira
• Jima
• Dukanci
Sana’o’in kasuwanci da hidima
• Kasuwanci
• Fatauci
• Ƙwadago
• Aikatau
• Wanki da guga
• Malanta
Sana’o’in zamani
• Gyaran waya
• Cajin waya
• Saidar layi da yin rijista
• Saidar data da kati
• Ayyukan kwamfuta (Computer)
• Buga takardu (Printing)
• Welding
• POP
• Plumbing
• Wayoyin lantarki
• Yin sabulu
• Yin Vaseline
• Ayyukan gine-gine da sauransu
Ya ku matasa, ku sani cewa rayuwa ba ta jiran mai sakaci. Duk sana’ar da ta halatta, komai ƙanƙantarta, tana da daraja. Ka fara da abin da kake da shi, ka haƙura, ka jajirce, Allah zai sa albarka. Kada ka raina sana’a saboda ƙanƙantarta, domin manyan mutane da dama da haka s**a fara. Gaskiya da Amana.
Allah ya albarka.
Allah yasaka da mafifincin alkairi malam ❤️🙏