03/09/2026
EMPOWERMENT GA MATASAN FAGGE: GINA MAKOMA, Ƙarfafa DOGARO DA KAI
Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Fagge Federal Constituency, Hon. Barr. Muhammad Bello Shehu Fagge, ya sake tabbatar da jajircewarsa wajen tallafa wa matasa da samar musu da hanyoyin dogaro da kai.
A wani sabon shirin tallafawa matasa, an raba baburan hawa da baburan Adaidaita Sahu ga wasu matasan Fagge, domin taimaka musu wajen fara ko bunƙasa sana’o’insu da inganta rayuwarsu.
Wannan ba rabon kayan taimako kawai ba ne; zuba jari ne cikin rayuwar matasa da tattalin arzikin Fagge.
Lokacin da matashi ya samu abin dogaro da kai, iyali na amfana, al’umma na amfana, kuma tattalin arziki na bunƙasa.
A faɗa a cika sai Hon. Muhammad Bello Shehu Fagge wakilci mai ma’ana, tallafi mai amfani, da aiki da ake iya gani.
©️ NAJIB SAYYADI