03/08/2026
Tambaya Gama'abota Ilimi naji wani malami yace auren mutu'a halal ne ga tambayoyina k**arhaka
TAMBAYOYI GAME DA FATAWAR PROF. MAQARI AKAN AUREN MU'AKKAD!!!
1). Su wadan nan ma'aurata na Mu'akkad zasu iya GADON JUNA, wato, matar zata iya gadon miji idan ya mutu hak**a mijin zai iya gadon matar idan ta mutu?
2). Matar zatayi takaba wa mijin idan ya mutu kuma menene adadin watanni/kwanakin takabar?
3). Idan aka samu haihuwa a yayin wannan irin auren, 'yayan suna da gadon 'ubansu'?
4). Ko mata ko matan da shi wannan matafiyin mai neman gujewa ZINA ya bari a gida suma akwai fatawar da za'a basu na samun irin tasu auren domin gujewa wa ZINA?
5). Wadansu muhimmman abubuwa ne s**a bambanta Auren Mut'ah da Mu'akkad?