AL-Furqan Islamic Foundation

AL-Furqan Islamic Foundation Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from AL-Furqan Islamic Foundation, Marketing Agency, ukashatugaladima2019@gmail. com, Kano.

30/11/2023

*_⬛️HASSADA⬛️_*

Darasi na ❶

*◼️Hassada shi ne: ka yi gurin gushewar wata ni'ima dake wajen ɗan uwanka, ba tare da ta dawo gareshi ba.*

◻️Allah maɗaukaki ya ce
*﴿نَحْنُ قَسَمْنَا بَيْنَهُم مَّعِيشَتَهُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ۚ وَرَفَعْنَا بَعْضَهُمْ فَوْقَ بَعْضٍ دَرَجَاتٍ لِّیَتَّخِذَ بَعۡضُهُم بَعۡضࣰا سُخۡرِیࣰّاۗ وَرَحۡمَتُ رَبِّكَ خَیۡرࣱ مِّمَّا یَجۡمَعُونَ}*
*"Mu ne muke raba musu abinchinsu arayuwar duniya, kuma muka ɗaukaka sashinsu akan sashi da darajoji, don sashinsu ya riƙi sashi amatsayin 'yan ƙwadago. Rahamar Ubangijinka ita tafi alkhairi daga abin da suke tattarawa".*
الزخرف 32

*💡Wani daga cikin magabata yana cewa "Na lura da Hassada, sai na gane cewa lallai dukkan rabo daga Allah yake, don haka ba zan yiwa kowa Hassada ba har abada".*

◻️Allah maɗaukaki ya ce
*(وَلاَ تَتَمَنَّوْاْ مَا فَضَّلَ اللّهُ بِهِ بَعْضَكُمْ عَلَى بَعْضٍ لِّلرِّجَالِ نَصِيبٌ مِّمَّا اكْتَسَبُواْ وَلِلنِّسَاء نَصِيبٌ مِّمَّا اكْتَسَبْنَ وَاسْأَلُواْ اللّهَ مِن فَضْلِهِ إِنَّ اللّهَ كَانَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمًا*
*"Kada ku riƙa gurin abin da Allah ya fifita sashinku akan sashe, maza suna da rabo daga abin s**a samu, mata ma suna da rabo daga abin da s**a samu. Ku roƙi Allah daga falalarsa. Lallai Allah yakasance mai ilimi ga dukkan komai".*
النساء: 32

◻️ Manzon Allah ﷺ ya ce
*🔺"Kada kuyi Hassada, kada kuyi kore, kada kuyi ƙiyayya kada ku ruɗi junanku....".🔺*
📜رواه مسلم ( 2559 )

◻️قال ابن بطال-رحمه الله- :
*"Aciki akwai hani game da Hassada akan ni'ima. Haƙiƙa Allah ya hana bayinsa masu Imani su riƙa yin gurin abin da ya fifita sashinsu akan sashi, sai ya umarcesu da su roƙeshi daga falalarsa".*
📜شرح صحيح البخاري 9/258

◻️قال ابن تيمية -رحمه الله- :
*Abin nufi, lallai ita Hassada wani ciwo ne daga cikin ciwukan zuciya, kuma ciwone da galibin mutane basa kuɓuta daga gareta sai 'yan kaɗan daga cikin mutane. Don haka ne ake cewa: Jiki baya kuɓuta Da Hassada, sai dai, Wawa shi yake bayyana ta, Karimi kuma shike ɓoye ta".*
📜الفتاوى 10 / 124

◻️قال ابن عثيمين -رحمه الل

30/11/2023

SANYA LAYA SHIRKA NE

Rataya layya ta zare,ko ta tsirkiya,ko ta abin wuya,ko wasu abubuwa a jiki,a mota, ko a gida da sauransu, da nufin suna tunkoɗewa mutum cutarwa daga mummuna ko kuma su kawo masa amfani,to yin hakan shirka ne ga Allah.

📌An karbo daga Uqba bn Amer Allah Ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah SAW yace:
*(Wanda ya sanya layya ya yi shirka)*
@السلسة الصحيحة(٤٩٢)

������������

An karɓo daga Abdullahi Dan Mas’ud Allah Ya yarda da shi ya ce: “Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare yace:
*(Ruqyah da layya da tiwala shirka ne)*
@📚 Sahih Al-Jami' (1632)

📌Ibn Mas'ud Allah Ya yarda da shi ya shiga wajen Wasu daga cikin iyalansa,sai yaga ta rataya laya,sai ya yanke layar ya cirata, sannan ya ce: *"Mutanen gidan Ibn Masud sun barranta daga shirka" *.
@📖Al-Jami’ na Ibn Wahb (681)

������������

📌Uqba bin Aamer Al-Juhani – Allah ya kara masa yarda – yana cewa dangane da layya:
*"Duk inda mutum ya sanya shi,to shi shirka ne" *
@📚 Al-Jami' na Ibn Wahb (682)


Allah ne mafi sani

30/11/2023

_🌹🌹An Kar6o Daga Abdillahi Bn Amr R.A Yace :Manzon Allah S.A.W Yace:"Ya Ishi Mutum Girman Zunubi Yana Tozarta Da Wanda Ya Wanda Yake Ciyarwa"🌹🌹_

_🌹🌹Manzon Allah S.A.W Yace : Idan Dayanku Yayi Fushi,To Yayi Shiru.🌹🌹_

Ahmad Ya Rawaito,Albany Ya Inganta.

*▶️Yana Daga Abinda Aka Shar'anta Yayin Fushi, Mutum Yayi Ta'awizi, Idan Da Hali Yayi Alwala, Ya Zauna Idan A Tsaye Yake, Yayi Shiru Idan Magana Yake, Har Sai Zuciyarsa Ta Samu Nutsuwa.*

*🔸Yin Addu'a Bayan Cin Abinci.🔸*

_🌹🌹An Kar6o Daga Abu Umamatal Bahily R.A Yace : Haqiqa Ma'aiki S.A.W Ya Kasance Idan Ya Gama Da Kwanon Abincinsa Sai Yace : Alhamdulillahi Kathiran, Dayyiban, Mubarakan Fihi, Gairu Makfiyyin Wala Muwadda'in, Wala Mustagnan Anhu,Rabbana.🌹🌹

https://www.facebook.com/profile.php?id=61553930797037&mibextid=rS40aB7S9Ucbxw6v

https://chat.whatsapp.com/Dg2bHpHnIGt5VfCwI0Ldhd

Marketing agency

29/11/2023

Marketing agency

29/11/2023

Assalamu Alaikum Warahmatullah wabarakatuhu

Muna gayyatarku Zuwa Wannan dandali Mai Albarka

Marketing agency

29/11/2023

Assalamu Alaikum warahmatullah

Address

Ukashatugaladima2019@gmail. Com
Kano

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AL-Furqan Islamic Foundation posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share