26/03/2025
ADDU'A
Ya ubangiji kasanya Qur'ani ya zamto mai ceton mu, ya ubangiji kasanya Alqur'ani ya cecemu ranar tashin Qiyama,
ya ubangiji kabamu lada cikin abinda mukeyi na ibadodi kakarɓi azumin mu, da ƙiyamul lailin mu, da Addu'oin mu, yan kasuwar mu ubangiji kasamusu imani cikin zukatansu, kasa musu son adalci da gaskiya cikin zukatansu Jami'an gomnatin mu ubangiji kasa musu imani cikin zukatansu, kasa musu adalci da gaskiya cikin zukatansu,
Dukkan wani wanda yake mai sana'a ko wanene Allah ya haɓaka sana'ar sa, mai aiki Allah ya albarkaci aikin sa.
Sunnah tv