Mafitar Arewa

Mafitar Arewa Shafin da yake kawo muku abubuwan da suke faruwa a Arewa.

03/09/2024

Garuruwa da dama a Najeriya sun wayi garin Talata da karin farashin man fetur.

Rahotanni sun nuna cewa a wasu wuraren lita daya ta kai naira 1500.

Yaya lamarin ya ke a naku garuruwan?

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince a zuba naira triliyan kusan 7 wajen biyan tallafin man fetur daga watan Ag...
19/08/2024

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince a zuba naira triliyan kusan 7 wajen biyan tallafin man fetur daga watan Agustan shekarar 2023 zuwa Disambar shekarar nan. Rahotanni sun ce tun a ranar 6 ga watan Yunin wannan shekarar shugaban ya amince a biya tallafin. A farkon wannan wata ne wasu daga cikin jama'ar kasar cikin fushi s**a gudanar da zanga zangar adawa da rashin shugabanci na gari da kuma tsadar rayuwa, abinda ya kai ga rasa rayuka.

📷Presidency

Yanzu - Yanzu Bababn Sifetan Yan Sandan Nigeria Kayode Egbetokun, ya umarci Kwamishinan Yan Sandan Birnin Tarayya Abuja ...
31/07/2024

Yanzu - Yanzu

Bababn Sifetan Yan Sandan Nigeria Kayode Egbetokun, ya umarci Kwamishinan Yan Sandan Birnin Tarayya Abuja da ya Ya Gudanar da bincike Tare da Kawo masa Rahoton binciken Abinda s**a gano akan Abinda akayiwa Dan Siyasa abdulmajid Dan Bilki Kwamanda

A Ranar 19 ga Watan Nan da Muke Ciki ne Dai Dan Gwagwarmaya Mai Kare Hakkin Dan Adam Muhammad Lawal Gusau, Ya Runutawa Bababn Sifetan Yan Sandan Nigeria korafi akan Cin zarafi da akayiwa Dan Bilki Kwamanda.

Idan za a tuna dai awani Bidiyo Abaya bayan nan anga Yadda Da ba akai ga gano ko suwaye ba, s**a Ci zarafin Dan Bilki Kwamanda ta Hanyar daure masa Hannu tare da Zaneshi da bulala.

A takardar da Bababn Sifetan Yan Sandan ya aikewa Kwamishinan Yan Sandan Birnin Tarayya Abuja, inda anan ne Lamarin ya faru, ya Bukaci Samun bayanin Abinda binciken ya gano Kafin Ranar 8-08-2024 Wato Watan gobe na Augusta Mai Zuwa.

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban wata ƙungiya da ita ma taso tabi sahun ƙungiyoyiɲ Arewa dómin shíga ząńga-ząńga ya janye bayaɲ ya...
23/07/2024

DA ƊUMI-ƊUMI: Shugaban wata ƙungiya da ita ma taso tabi sahun ƙungiyoyiɲ Arewa dómin shíga ząńga-ząńga ya janye bayaɲ ya gana da ɗan gidan Shugaba Tinubu sannan sai ya fahimci céwa akwai tuggu a cikin zãɲga-ząɲgar ta lumana da wasu zasu jagoranta, shi yasa ya janye batun shigar ƙungiyar su wànnañ zaɲga-zaɲgâ.

Me zaku ce?

Daga Comr Abba Sani Pantami

YANZU-YANZU: Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya Ta Sanar Da Haŕamťa Źañģa-Źànģar Da Ake Shirin Yi Kan Tsadar RayuwaShugaban '...
23/07/2024

YANZU-YANZU: Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya Ta Sanar Da Haŕamťa Źañģa-Źànģar Da Ake Shirin Yi Kan Tsadar Rayuwa

Shugaban 'yan sandan na kasa, Kayode Egbetokun ne ya bayyana hakan, a yayin wata ganawar da ya yi da wasu jami'ansa.

Me za ku ce?

Babban Bankiɲ Najeriya CBN Ya Ƙara Kuɗin Ruwa Zuwa Kaso 27.67 Cikin ƊariA watan mayun da ya gabata ne CBN ya ƙara kuɗin ...
23/07/2024

Babban Bankiɲ Najeriya CBN Ya Ƙara Kuɗin Ruwa Zuwa Kaso 27.67 Cikin Ɗari

A watan mayun da ya gabata ne CBN ya ƙara kuɗin ruwan da kaso 26.25%.

Me zaku ce?

Tirka-tirkar Dangote da gwamnatin tarayya.Na saurari wata hira da a ka yi da wani masani a kan harkar mai wato Kevin Ema...
22/07/2024

Tirka-tirkar Dangote da gwamnatin tarayya.

Na saurari wata hira da a ka yi da wani masani a kan harkar mai wato Kevin Emannuel, wanda ya yi fashin baki a kan turka-turkar da ke tsakanin gwamnatin Najeriya da kamfanin mai na Dangote. Babban abinda hirar ta nuna shi ne cewa gwamnatin Najeriya ba ta shirya kawo gyara a kan matsanancin halin da Najeriya ta ke ciki ba.

Da farko dai wannan kamfani na mai na Dangote an gina shi ne bisa yarjejeniyar cewa gwamnatin Najeriya zata baiwa Dangote danyen mai na wani adadi da idan an bashi wannan adadin ita kuma gwamnati za ta mallaki kaso 20 cikin 100 na hannun jarin kamfanin.

Sai dai saboda yawan basuss**a da gwamnati ta karba wanda ta ke biyansu da danyen mai ya sa gwamnati ta kasa biyan Dangote wannan adadin kudin. Hakan ne ya sa Dangote ya yanke shawarar cewa zai rika sayo danyen mai daga kasashen waje, wanda idan ya tace su ya sayar a kasashen waje sai ya fi cin riba a kan ya sayar da su a Najeriya.

Wannan abu ya batawa gwamnatin tarayya rai kuma ya baiwa masu sana'ar shigo da mai daga kasashen wajen shiga su fita su kara yamutsa al'amarin.

Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar cewa man da Dangote ya ke fitarwa ba shi da inganci (a ma'aunin Octane da Sulphur level), duk da kuwa cewa ita gwamnati ba ma ta da injinan yin wadannan gwaje-gwaje ballantana ta iya yanke wannan hukuncin.

Dadin dadadwa, gwaji da aka yi a kan idon yan majalisa a matatar man Dangote ya nuna cewa yawan sulphur na man Diesel na kamfanin Dangote baiwa wuce 80 ppm ba (baa so ya wuce 200 ppm idan man cikin gida ne). Ma'ana dai mai ne mai inganci sosai. Sannan Dangote ya ce zuwa August zaa ci gaba da tace man har sai ya kai 10 ppm (adadin da a duniya ma kaf matatu kadan ne su ke iya tace man su ya kai haka).

Dangote ya ce kuma an gwada man da a ke sayarwa yan Najeriya a kamfaninsa ya na da sulphur (sama da ppm dubu daya [1000 ppm]). Abin takaicin shi ne wannan adadin sulphur yawansa ya kai yawa, kuma hatsari ne sosai ga lafiyar al'umma. Amma a haka a ke sayarwa da yan Najeriya shi. A takarda adadin sulphur din da ake rubutawa daban. Idan kuma an yi gwaji adadin da zaa gani daban.

Dangote ya kalubalanci majalisa a kan cewa su gayyaci manyan kamfanunuwa na duniya masu gwaje-gwaje su gwada man kamfaninsa da kuma man da a ke sayarwa da yan Najeriya a kasuwa.

Abin takaicin shi ne daga karshe haka gwamnati zata bari a ci gaba da sayarwa da mutane gurbataccen mai. Sannan a ci gaba da biyan kudin subsidy daga aljihun gwamnati don sayen shi wannan gurbataccen man.

Allah ya kyauta.

Abdulaziz T Bako

Shugaba Tinubu ya amince da Naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya.Shin kuna ganin wannan mataki zai r...
18/07/2024

Shugaba Tinubu ya amince da Naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya.

Shin kuna ganin wannan mataki zai rage wa ma'aikata radadin tsadar rayuwa?

Nawa kuke ganin ya cancanci a biya a matsayin mafi karancin albashi a Najeriya?

Address

No 129 Katsina Road
Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mafitar Arewa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share