Funtua Zone Reporters

Funtua Zone Reporters Muna Maku Barka da zuwa shafinmu Domin samun labaran Duniya kasance da jaridar Funtua Zone Reporters
(1)

Marafan Dandume ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar matar shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin KatsinaMai Girma Alhaji La...
15/04/2026

Marafan Dandume ya aike da sakon ta’aziyyar rasuwar matar shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Katsina

Mai Girma Alhaji Lawal Ibrahim Danmumuni (Marafan Dandume)” shugaban ƙungiyar MARAFAN DANMUMUNI SUPPORT DIKKO 2027 Ya aike da saƙon ta’aziyya ga shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Jihar Katsina, bisa rasuwar matarsa, Hajiya Maijidda Abdulkadir Mamman Nasir Andaje.

Marigayiyar ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya, lamarin da ya jefa iyalanta da ma al’umma cikin alhini.

A cikin saƙon ta’aziyyar da ya fitar, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi, yana mai jajanta wa mijinta da sauran iyalai da abokan arziki, tare da addu’ar Allah ya jikanta da rahama, ya gafarta mata kura-kuranta, ya kuma ba waɗanda ta bari haƙurin jure wannan rashi.

Haka kuma, ya miƙa gaisuwa da ta’aziyyarsa ga Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, da ma’aikatan fadar gwamnatin jihar, bisa wannan rashi da ya shafi gwamnati da al’umma baki ɗaya.

,AYYUKAN SANATA MUNTARI MOHAMMED DANDUTSE (KASHI NA 2)Rawar da ya taka wajen inganta ilimin manyan makarantu a NijeriyaS...
11/04/2026

,AYYUKAN SANATA MUNTARI MOHAMMED DANDUTSE

(KASHI NA 2)

Rawar da ya taka wajen inganta ilimin manyan makarantu a Nijeriya

Sanata Muntari Mohammed Dandutse, wakilin mazabar Katsina ta Kudu a Majalisar Dattawan Nijeriya, na daga cikin sanatocin da ke taka muhimmiyar rawa wajen inganta ilimin manyan makarantu a ƙasar.

Wannan rawar gani ta ƙara fitowa fili ne tun bayan naɗa shi a matsayin Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Manyan Makarantu da Asusun Tallafa wa Ilimi na Manyan Makarantu (TETFund).

1 Ƙara Harajin Ilimi:
Sanata Dandutse ya goyi bayan ƙarin harajin ilimi daga kashi 2.5 zuwa kashi 3 cikin ɗari, matakin da ake sa ran zai ƙara kuɗaɗen bincike, samar da kayayyakin more rayuwa, da kuma rage gibin da ake samu a wasu manyan makarantu.

2 Kafa Sabbin Jami’o’i:
Ya gabatar da kudurori na kafa sabbin jami’o’in tarayya a sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da:

Jami’ar Tarayya ta Sufuri a Daura

Jami’ar Tarayya ta Kimiyyar Lafiya a Funtua

Jami’ar Tarayya ta Ilimi (Fasaha) a Gombe

Manufar hakan ita ce rage gibin rabon cibiyoyin ilimi tsakanin yankuna da kuma ƙara damar samun ilimi.

3 Dokar Rancen Ɗalibai:
Kwamitin da yake jagoranta ya taka rawa wajen amincewa da Dokar Rancen Ɗalibai ta 2024, wadda ke bai wa ɗalibai marasa galihu damar samun rancen karatu ba tare da riba ba.

4 Inganta Fasahar ICT Sanatan ya nuna damuwa kan gibin fasahar sadarwa, inda ya bayyana shirin gina cibiyoyin ICT a dukkan ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya cikin kasafin kuɗin shekarar 2026. Ana sa ran wannan zai sauƙaƙa harkokin dijital da jarrabawa irin su UTME, musamman a yankunan karkara.

5.T Sanata Dandutse ya tallafa wa matasa da dama daga yankin Funtua da guraben karatu, Aiki a matakai Daban daban Sama da matasa 80 Sun Amfana

6 Sa ido da tabbatar da inganci Ziyarce-ziyarce zuwa Makarantu A ƙarƙashin jagorancinsa, kwamitin ya gudanar da Ziyarce-ziyarce zuwa jami’o’i, polytechnics da colleges of education domin duba ayyukan gine-gine, dakunan gwaje-gwaje da dakunan karatu da TETFund ke daukar nauyi.

7 Zaman Sauraron Bayani (Oversight) karkashin Kwamitin Sanata ya gudanar da zaman sauraron bayanai tare da shugabannin TETFund domin tantance yadda ake raba da kashe kuɗaɗe tare da ƙarfafa gaskiya da riƙon amana.

8 Ƙarfafa Ilimi da Bincike Tallafa wa Horar da Malamai da Bincike Kwamitin ya mayar da hankali wajen inganta horar da malamai da bincike domin bunƙasa ilimi da ƙirƙire-ƙirƙire a Nijeriya.

Za a muci gaba da kawo muku sauran ayyukan da Maigirma Sanata Muntari Dandutse yayi a fannoni daban-daban.

Dandutse Media Reporter

Tata ya wallafa labarinsa da duk mai tausai dole ya zubda masa hawaye  in ya karanta labarin har karahe 😭Ya bayyana yadd...
09/04/2026

Tata ya wallafa labarinsa da duk mai tausai dole ya zubda masa hawaye in ya karanta labarin har karahe 😭

Ya bayyana yadda a yanzun ba shi da gida ko daya, sai gidan haya, abin akwai ban tausai sosai

"KADAN DAGA CIKIN LABARI NA DA KUMA MATSAYA TA A SIYASAR 2027

Lokacin da ta kira ni, ban dade daga tashi daga barci ba. Kanwata ce ta 6angaren mahaifiyata. Mu kan jima bamu gaisa ba, amman tana da kokarin ganin cewa zumuncin dake a tsakanin mu bai yi rauni ba. Na amsa wayar nace Amina kina lafia tace lafia lau. Yaya gidan ya iyali? Duka alhamdulillahi. Babu abinda ya fito bakin ta sai take ce mani ni dai wallahi sau biyu ina mafarkin ka kuma bani jin dadin yanda nike ganin ka a cikin mafarki. Duk rai yana son yaji magana mai dadi ko da kuwa karya ce. Magana irin wannan tana da sosa rai. Nace Amina yaya k**e ganina a cikin mafarki? Tace wallahi sau biyu ina ganin ka kwance kana barci ka lullu6e da tsumman bargo, ga wasu bayin Allah nan cikin fararen kaya suna son su iso wajen ka amman abin ya gagara. Tace ita kuma a dan sanin da tayi tsumman bargo alama ce ta talauci. Subhanallahi! Bacin ta gama ni kuma na tabbatar mata cewa talauci kam ina fama dashi sai dai abinda Allah yayi daga cikin rahamar shi. A lokacin gidaje biyun da nike zaune ni da iyali na duk na haya ne kuma hayar ta kare, masu gidajen sun azabtar dani in tashi in basu gidajen su tunda na kasa sabunta hayar. Babu kudin da zan biya kuma babu inda zan samo su. Daya daga cikin su ma har ya kai ni kotu kuma kotu ta bani wa'adin tashi. Wannan duk ya biyo bayan asarar duk wani gida nawa da na mallaka a rayuwa, in ban da guda daya dake a Dutsinma, wanda shima a cikin garari yake a lokacin. Bani da kudin biyan hayar kuma bani da inda zani je a biya mani. Wata sa'a inyi kuka ni kadai cikin duhu ba tare da iyali sun sani ba, saboda na san irin cin mutunci da wulakancin da ake fuskanta in kotu zata fitar da kai daga cikin gida, na ga wannan wulakancin a kan gidaje na biyu da nayi asarar su kuma ina tausaya ma iyali na da kara fuskantar irin wannan tozarcin da wulakancin. Wata sa'a kuma ni kadai sai in taushi kaina in ba kaina kwarin gwiwa cewar duk mai bayar wa, sai dai jarabawa, amman Allah ba zai ta6a hana shi ba. Masallaci a lokacin sai ya zamo wurin da nafi sha'awar zama a rayuwa ta.

Amina tace, bayan tabbatar mata da nayi na halin rashin da nike ciki ba tare da bata wani labari ba, tunda bani zaton tana da taimakon da zata iya yi mani, da zani amince da ta hada ni da wani mutum watakila, cikin yardar ubangiji a sami taimako ta wajen shi. Irin wadannan maganganun anyi mani su a rayuwa babu adadi amman bani yarda dasu saboda na san komai rubutacce ne daga Allah kuma dan Adam baya da abinda zaya iya yi mani sa6anin abinda Allah ya kaddara mani. Amman a wannan ranar, cikin taimakon Allah, a karo na farko, sai na amince mata da ta hada ni da mutumen. Dalili kuwa ina son kauce ma masu zargi da zagi na da cewa ni bani daukar shawara duk da bani da tunanin wani alkhairi a cikin abin. In har sihiri ne, k**ar yanda wasu s**a sha fadi, particularly masu raunin imanin cewa wannan abin ba na Allah da Annabi bane, to na rufe bakin su. Babu sauran zargi a tsakani. Bugu da kari sihiri gaskiya ne, tsafi gaskiya ne, kuma ni ba kowa bane, don fiyayyen halitta ma, Annabi Muhammad SAW, anyi mashi kuma ya k**a shi, to ballantana ni? In kuma ba shi bane ba, to addu'a abin so ce daga kowane irin dan Adam saboda ban san irin baki da darajar da Allah yayi ma shi ba. A sanadiyyar haka ne na shiga wata sabuwar rayuwa da Malamin da Amina ta hada ni da shi. Mutum ne kamili, mai ilimi na addini da zamani, mai tsoron Allah kuma mai tsaya ma gaskiya.

Watau wanda duk yace maka babu sihiri ko tsafi to kawai bai ta6a zama victim na matsafan bane, ko kuma ko da ya zamo to Allah bai haska mashi shi bane ballantana ya gane. Sihiri gaskiya ne, tsafi gaskiya ne. Ni Tata victim ne nasu daga dan abinda Allah Ya bayyana mani a kan kai na. A kai na an bizne bakin doki da rai a tsohuwar makabarta ta Unguwar kudu a Dutsinma. A kai na an kashe makaho an baiwa macijiya shi ta hade shi da layu duk don kada in sami biyan bukata a rayuwa. A kaina an fitar da sabuwar gawa daga cikin kabari an cire mata kwanya an cika ta da layu an maida ta an bizne don in haukace. Ban da bakaken shanu, jakuna, macizai da karnuka ba iyaka da aka yi amfani dasu. Duk wannan anyi ne kawai don in yi asarar damar da nike da ita ta taimakon al'umma da addinin Allah da kuma tsoron kada inyi gwamnan Katsina.

Kafin 2011 ni ba dan siyasa bane. Ni maaikacin gwamnati ne kuma babu abinda nike ji ma dadi, nike so irin aiki na. Kishin karamar hukumuta ta Dutsinma da son nuna godiya ga gwamnan dake ci a lokacin, Ibrahim Shehu Shema, a kan ayyukan ci gaba da naga yayi a jihar, ya sanya na shigo siyasa domin in k**a ma shi yaci second term. Ba don komai ba sai don fadar Allah cewa babu sak**ako ga aiki kyakkyawa face alkhairi. Saman wannan, ina kuma da kwadayin in ya samu nasarar second term, to ya zamanto encouraged by nasarar da ya samu ya kara lunka alkhairi a jihar saman abinda yayi. Bacin wannan bani da wani dalilin da yasa na shigo siyasa. Amman Allah dake tsara rayuwa yanda yaso, sai gashi wannan gudummuwa dana shigo in bada, ta jawo mani zama a cikin siyasa harda takara ta gwamna, abinda bani sha'awa a lokacin kuma ban ta6a tunanin ta ba, wanda taja har ta kai na rabu da aikin nan wanda nafi so saman komai.

Abinda duk ya faru ya faru a 2015 wanda tun daga lokacin ne rayuwa ta ta canza. Nayi kokarin komawa bakin aiki na amman sau goma sha biyu ina rubuta takardar janye takardar retirement dina amman duk lokacin da aka fara aiki a kan takardar tawa sai file din nan ya 6ace, ko sama ko kasa ba za a kara ganin shi ba. Cikin wannan lokacin ne na rasa gidaje na na koma haya. Na rasa motoci na na koma tafiya kasa. Na rasa masoya na na wannan lokacin sai dai wasu, wadanda su ban ma amfane su ba a lokacin da nike da shi ba, saboda ban san su ba, sune s**a tsaya mani. Na rasa duk wani mai taimako wanda zai iya tausaya mani in sami abin yi don tsare mutunci na. Harka koya take in na dauko ta sai anzo kusan 99% na nasara sai ta rushe a koma square one k**ar ba a ta6a yi ba. A cikin wannan halin ne Allah ya sa Amina ta kira ni, lokacin da sutura ta sawa ma tana neman ta gagare ni. Babbar godiya ta ga Allah ita ce a wannan lokacin ne Allah ya dauki rayuwar mahaifiya ta bata ga irin wulakanci da jarabawar rayuwar da na shiga ba. Ta bar duniya da tunanin dan ta jarumi ne kuma mai arziki!

Taimakon Allah na zuwa daga in dai rai bai ta6a zuwa ba haka ma zuciya bata ta6a tunani ba. Abubuwa da yawa sun faru, kuma allah ya bayyanar da abinda yaso daga cikin ikon shi. Na ga abin mamaki naga abin tsoro. A sanadiyyar haka na san ko wanene Allah. Wanda duk ya gaya maka ya san Allah to ya bari har Ya ta6a shi sannan zai san ko waye Allah. Amina da malam allah ya saka maku da alkhairi.

Malam ya wahala a kokarin taimaka mani. Ba sau daya ba ba sau biyu ba allah ke kubutar da malam a kan ido na. Yayi asarar lafiya a kan ido na, yayi asarar dukiya a kan ido na, yayi asarar abokanan huldar shi akan ido na, sannan a kan ido na za a halba malam ya bugo ceiling kafin ya dawo kasa yayi jina jina sannan ga wasu manyan lizards da ban ta6a ganin irin su ba sun k**a wuyan shi yana makarkatar mutuwa. Naga tashin hankali. Wanda rayuwa bata ta6a ba zai zaci tatsunniya nike.

Sannu sannu taimakon Allah yazo mamu ta6angaren da bamu zata ba.

Lokacin da nike hidima, kafin za6en 2015, ashe akwai shugaban da nayi ma laifi a jihar Katsina. A irin na shi tunanin, wai na shigo cikin siyasar shi, ba don komai ba, sai don nayi amfani da inuwar shi inyi suna sannan in raba shi da jama'a. Saboda haka ya dauki mataki kaina. Matakan guda biyu ne. Mataki na zahiri da mataki na badini. Matakin zahiri shine a raba ni da aiki na, saboda ai sai ina da aiki zani sami abin da zan ba jama'a da har suke bi na. A kan wannan anyi petitions babu iyaka zuwa wajen Head of Service of the Federation, Minister of Finance, Minister of Defence da kuma Secretary to the Government of the Federation. Wanda daga karshe da yaga bai sami nasarar da yake nema ba ya rubuta ma shugaban kasa Jonathan kuma ya dauka da hannun shi ya kai ma shi. Duka Allah ya kare ni babu inda ya sami biyan bukatar da yake so. Bacin wadannan petitions din, bai yi kasa a gwiwa ba sai da ya bini da petitions wajen jami'an tsaro: EFCC, ICPC, Code of Conduct Bureau da kuma Nigeria Police. Su ma dai Allah bai bani kunya ba don Ya tsaya mani. Haka aka yi su a banza sai dan kamun da akayi mani wanda nayi zaman cell na EFCC na sati 4.

Matakin badini kuwa shine aka bazu cikin malamai na tsubbu a kan yanda za a yi dani. A nan ne a ka dauki suna na aka kai ma wani shahararren matsafi mai bautar rana wanda ke a India. Bukatar guda 4 ce. Na farko dai a dauki rayuwa ta in bar duniyar kwata kwata. In haka bai yiwu ba, a raba ni da lafiya ta ya kasance ina duniya amman k**ar bani duniyar saboda ciwo ko lalacewa ta hauka ko wani abu mak**ancin haka. Ta ukku, a raba ni da duk wani abinda ake kira wadata ko samu, in rabu da abinda ke gare ni sannan duk wata kofa ko kafa ta samu a lalata ta yanda arziki sai dai in gan shi a wajen wasu ba dai in same shi ba. Ta karshe shine a raba ni da duk wani mai so na, a saka kyama ta a zukatan al'umma yanda babu wanda zai iya taimako na.

Ni ba wannan ne ya 6ata mani rai ba sai kasancewar a wannan bukatar ta shi ya hada da children dina cewa suma yana son kar suyi albarka a rayuwa domin sunana ya 6ace a bayan kasa ko bayan rai na. Wannan shine yafi yi mani zafi. In har ni akwai laifin da na yi mashi, in har akwai shi kenan, saboda ni taimakon shi nayi, to laifin me dan dana haifa yayi ma shi? Allah ya isa! Tun daga wancan lokacin har ya zuwa yau, akwai abinda yake aika ma shi wannan matsafin, bayan duk kwana 75 don biya ma baqaqen aljannun da s**a addabe ni bukata don kar in sami sukuni ko faraga a rayuwa har in koma ga mahalicci na.

Lokacin da suke kokarin raba ni da duk wata hanyar samun taimako ko masu taimakawa, sai Allah ya bar ni da talakkawa na. A duk ranar duniya ba a rasa talakka daya, namiji ko mace, da zai yi mani addu'a ta alkhairi da tausayawa, saboda talakkan jihar Katsina yana da yaqinin cewa samu na samun shi ne. Addu'ar su da kaunar su ita ta kawo har Allah ya tausaya mani ya tsare mani rayuwa ta, lafia ta da mutunci na sa6anin abinda wannan bawa Allah ya qudurta a kaina. Waraka kuma ta duniya, biiznillahi ina da yaqinin cewa Allah ba azzalumi bane kuma baya son zalunci, ba zai barni cikin wannan halin ba saboda wancan bawan na shi yaji dadi. Da yardar Allah wata rana sai na fita, sai an ga k**ar ba a ta6a yi ba.

Da dama ana ta magana a kan matsaya ta a siyasa, wanda har yasa wata sa'a ra'ayin zuciya yana neman ya rinjaye ni zuwa aikata abinda ba hali na ba. A rayuwa ba a ta6a yi mani alkhairi ban rama ba sai dai in bani da hali, ballantana in maida sharri. Wannan ba hali na bane. Duk wanda ya san Dikko Radda ya san shi da baya son abubuwa guda biyu. Na farko, Dikko baya son rabuwa da kudi ko kadan sai dole. Na biyu Dikko baya son a tanbaye shi kudi, to kun kau sa6a. Allah ya sani ina cikin mutane yan kadan dake karya wannan dokar ta Dikko kuma yayi mani ko baya so. Dikko yazo gida na ya baiwa iyali na N1.5m. Dikko ya biya ma yarinya ta dake a private university school fees lokacin da ake neman a kore ta saboda na kasa biya mata don bani dasu. Dikko ya bani N10m na biya muhalli ga iyali na a lokacin da dukkanin su suna gidajen iyayen su saboda bani iya biyan hayar. Dikko ya bani mota ta hawa sau biyu. In yi ma shi karya ya bani in gaya ma shi gaskiya ya bani ba sau daya ba sau biyu ba. Dalilin hakan ne yasa na sauko kasa nazo na fara yi ma shi program a gidan radio domin in nuna godiya ta a gare shi sannan in saka mashi kwatankwacin hali na. Saboda haka zan tsaya da Dikko, da dadi babu dadi har Allah ya kai mu ga nasara ya kammala wa'adin shi na biyu saboda shi kadai ne yayi mani irin wannan taimakon duk duniya a lokacin da bani da kowa sai Allah.

Tabbas a tare da shi akwai wadanda basu kaunata kuma in suna da iko ba zasu so in samu ko pure water ba ballantana wani matsayi. Zan yi hakuri in taimake shi daga nesa ba tare da na shige mashi ba har nima allah ya kawo mani tawa mafitar. Ba zani bar APC ba, ba zani yi fada da APC ba, hakazalika ba zani guji Dikko Radda ba. Masoya na da wannan matakin nawa ybai yi ma dadi ba ko ya 6ata masu rai ko yayi disappointing nasu, including a part of my family, ina neman afuwar su da kuma basu hakuri. I would rather die poor with a clean conscience than swim in opulence with a fractured ego. Inshaa Allahu ba zani bar ma diyana abin fadi ba a rayuwa.

Nagode kwarai?"

Tata

07/04/2026

Maigirma Gwamnan Jihar Katsina, Gwagwaren Katsina—wanda ina ka fito talaka, wa kake so, talaka, wanda kullum talaka yake so ya cigaba,

Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Umar Radda, ko kuma mu ce (Dikko Umar Dandume).”

Cewar Alhaji Lawal Ibrahim Danmumuni
(Marafan Dandume)” shugaban ƙungiyar MARAFAN DANMUMUNI SUPPORT DIKKO 2027 .

Tashin hankaliYan binda sun shiga garin Matazu da ranar nan tsaka, inda rahotanni s**a bayyana cewa har s**a kashe dan s...
05/04/2026

Tashin hankali

Yan binda sun shiga garin Matazu da ranar nan tsaka, inda rahotanni s**a bayyana cewa har s**a kashe dan sanda daya da jikkata wasu mutanen gari su biyu

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UNBarayin Daji Sun Zama Ajalin Matashi Babangida Babba Akan Hanyar Sabuwa.Allah Ya yi wa...
31/03/2026

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN
Barayin Daji Sun Zama Ajalin Matashi Babangida Babba Akan Hanyar Sabuwa.

Allah Ya yi wa wani matashi mai suna Babangida Babba rasuwa sak**akon harbin da wasu ‘yan bindiga s**a yi masa.

Lamarin ya faru ne a yau, yayin da marigayin ke kan hanyarsa ta zuwa kasuwar Sabuwa jihar Katsina, inda ake zargin ‘yan bindigar sun tare shi tare da bude masa wuta.

Majiyoyi sun bayyana cewa harbin da aka yi masa ya yi muni, wanda hakan ya yi sanadin rasuwarsa nan take kafin a kai shi asibiti.

Al’umma sun bayyana alhini da jimami kan wannan mummunan lamari, inda s**a yi addu’ar Allah Ya jikansa da rahama, Ya kuma ba iyalansa hakurin jure wannan rashi.

Allah Ya gafarta masa, Ya sa Aljannatul Firdausi ce makomarsa. Ameen.

Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin amsa tambayoyin manema labarai a wani faifan bidiyon da kafar yaɗa labarai ta Aljaz...
24/03/2026

Shugaban ya bayyana hakan ne a yayin amsa tambayoyin manema labarai a wani faifan bidiyon da kafar yaɗa labarai ta Aljazeera ta yaɗa wanda aka ɗauka a filin jirgin Jihar Florida da wakilan WAT News Hausa s**a samu.

Hakan na zuwa ne mintuna kaɗan bayan da shugaban ya sanar cewa ya ɗage shirin kai hari kan cibiyoyin lantarkin Iran saboda ya fara tattaunawa da ƙasar, iƙirarin da Tehran ta ƙaryata nan da nan.

'Yar Jarida: Shin wanene zai cigaba da sarrafa mashigin Hormuz bayan cimma yarjejeniya da Iran?

Trump: Za mu riƙa sarrafa mashigin Hormuz ne ta hanyar haɗaka, kuma wataƙila ni da Ayatollah ne za mu riƙa sarrafa shi, Inji Shugaban.

Shin menene ra'ayinku game da wannan?

📷/: Donald J. Trump/: Credit/[The WhiteHouse]

Iran Ta Sha Alwashin Kashe Netanyahu Yayin Da Hare-Hare S**a Girgiza Tel AvivDakarun juyin juya hali na Iran sun sha alw...
15/03/2026

Iran Ta Sha Alwashin Kashe Netanyahu Yayin Da Hare-Hare S**a Girgiza Tel Aviv

Dakarun juyin juya hali na Iran sun sha alwashin kashe Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, a daidai lokacin da rikicin da ke tsakanin ƙasashen biyu ke ƙara tsananta.

Rahotanni sun ce hare-hare masu ƙarfi sun kai har tsakiyar Isra’ila, inda aka rika jin ƙarar fashe-fashe a tsakiyar birnin Tel Aviv da sanyin safiyar ranar Lahadi.

Sai dai hukumomin Isra’ila sun bayyana cewa tsarin tsaron su ya samu nasarar tare yawancin mak**an da aka harba daga Iran kafin su kai ga muhimman wurare.

Duk da wannan ikirari na Isra’ila, wasu faifan bidiyo da s**a bazu a kafafen sada zumunta sun nuna yadda hare-haren s**a haddasa ɓarna mai yawa a wasu sassan ƙasar.

Lamarin ya ƙara tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, yayin da ake fargabar rikicin na iya ƙara faɗaɗa idan ba a samu sassauci tsakanin ɓangarorin ba.

Funtua zone Reporter

Zafafan hare-haren Iran sun lalata Sansanin sojin isa dake Baharain. Abdul Journalis TV
15/03/2026

Zafafan hare-haren Iran sun lalata Sansanin sojin isa dake Baharain.

Abdul Journalis TV

Ga halin da birnin Tel Aviv ke ciki a daren yau bayan hare-haren mak**ai masu linzami
15/03/2026

Ga halin da birnin Tel Aviv ke ciki a daren yau bayan hare-haren mak**ai masu linzami

Rikici ya ɓarke tsakanin shugabar ALGON da Alhassan Ado bayan rasuwar jami'in tsaro a wajen "rabon shinkafa" Rikicin da ...
14/03/2026

Rikici ya ɓarke tsakanin shugabar ALGON da Alhassan Ado bayan rasuwar jami'in tsaro a wajen "rabon shinkafa"

Rikicin da ke ruwa tsakanin shugabar karamar hukumar Tudun Wada kuma shugabar ƙungiyar kananan hukumomi ta Jihar Kano (ALGON), Hajiya Sa’adatu Salisu da dan majalisar wakilai mai wakiltar Doguwa da Tudunwada, Alhassan Ado Doguwa ya fito fili.

Daily Nigerian Hausa ta gano cewa rikicin ya baiyana ne sak**akon rasuwar wani jami'in hukumar tsaron fararen hula, wato Civil Defense a yayin taron rabon shinkafa da kudade da Alhassan Ado ya shirya a Tudunwada.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa jami'in, wanda kawo yanzu ba mu samu sunan sa ba, ya rasu ne bayan an kawo su don tabbatar da zaman lafiya a wajen taron.

Sai dai kuma a wani sako da wallafa a shafin ta na Facebook, Hajiya Sa'adatu ta zargi Alhassan Ado da hannu a kisan jami'in tsaron, inda har ta yi kira ga shugaban ƙasa da ya shiga maganar don ganin an yi hukuncin da ya dace.

A sakon, Sa'adatu ta yi kira ga gwamnatin Tltarayya da ta Jihar Kano da su gaggauta shiga lamarin da ya faru a Tudun Wada domin tabbatar da adalci da kare rayuka da mutuncin al’umma.

Ta kuma yi kira da a dakatar da Hon. Alhassan Ado Doguwa daga duk wasu harkokin siyasa da tarurruka har sai an kammala binciken da ake buƙata.

Ta ce rasuwar matashin babban rashi ne ga iyalansa da al’ummar yankin baki ɗaya, inda ta yi addu’ar Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa, tare da bai wa iyalansa, abokansa da daukacin al’ummar Tudun Wada ƙarfin jure wannan babban rashi.

Hajiya Sa’adatu ta jaddada cewa al’umma ba za su ci gaba da kallon irin waɗannan abubuwa na rashin tsaro da asarar rayuka ba tare da ɗaukar matakin da ya dace ba.

Sai dai kuma a nasa martanin, Alhassan Ado ya baiyana takaici kan kisan, inda shi ma ya yi kira ga hukumomin da su ka dace da su gudanar da bincike akan lamarin.

Sai dai kuma Doguwa, wata sanarwa da ya sanya wa hannu ya kuma fitar ga manema labarai, ya nuna bacin ran sa ga wasu maganganu da su ke danganta shi da kisan.

A dan haka, Doguwa ya ci alwashin ɗaukar matakin shari'a ga duk wanda ya ke masa ƙage don kawai don haddasa fitina a Tudunwada.

"Ni, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ɗan majalisa mai wakiltar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, 13/03/2026, bayan kammala taro da muka gudanar na rabon tallafin kayan azumi da na Sallah ga al’ummar ƙaramar hukumar Tudun Wada mata da maza.

" Amma daga baya na samu labarin cewa wasu bata gari sun yi yunƙurin tayar da tarzoma a wurin rabon kayan, lamarin da ya yi sanadin rasuwar wani jami’in tsaro na Civil defence.

"Ina miƙa ta’aziyyata ga Hukumar tsaro ta Civil Defence, iyalansa, da kuma al’ummar ƙaramar hukumar Tudun Wada baki ɗaya. Allah Ya jikansa da rahama, Ya gafarta masa. Ameen.

" Zan yi amfani da wannan dama nayi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda s**a haddasa wannan tashin hankali, tare da ɗaukar matakin da ya dace a kansu bisa doka.

" A ƙarshe, ina jan hankalin waɗanda suke yaɗa labaran ƙarya da kalaman batanci da suke alakanta ni kai tsaye da wannan abinda ya faru cewa za mu ɗauki dukkan matakan doka da s**a dace domin kare mutuncinmu da na al’ummar ƙananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada.

"Shi kuma Allah Ya jikansa Ya masa rahama. Ameen," in ji Doguwa.

An gudanar da jana’izar mutane 15 da s**a rasa rayukansu sak**akon harin ‘yan bindiga a garin Ɗansoda da ke cikin Ƙarama...
11/03/2026

An gudanar da jana’izar mutane 15 da s**a rasa rayukansu sak**akon harin ‘yan bindiga a garin Ɗansoda da ke cikin Ƙaramar Hukumar Ɗandume a Jihar Katsina.

Rahotanni daga yankin sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne cikin daren ranar Talata, inda s**a shigo garin ɗauke da manyan mak**ai. Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun riƙa harbe-harbe kan mai uwa da wabi, lamarin da ya jawo mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu.

Wasu mazauna yankin sun ce maharan sun shafe lokaci suna cin karensu babu babbaka a cikin garin kafin daga bisani su tsere.

Bayan harin ne aka gudanar da jana’izar mutanen 15 da aka kashe, inda al’ummar yankin s**a taru cikin jimami domin yi musu addu’ar rahama.

Funtua zone Reporter

Address

Katsina Ala

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Funtua Zone Reporters posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Funtua Zone Reporters:

Share