Katsina Trends

Katsina Trends Follow us for more Exclusive Contents
Katsina and beyond
DM for Collabs and Promo

🚨 SPECIAL OFFER FOR ALL VENDORS!  50% OFF STALL PRICES + REGISTRATION EXTENDED!Assalamu Alaikum, Dear Vendors,We listene...
21/08/2026

🚨 SPECIAL OFFER FOR ALL VENDORS! 50% OFF STALL PRICES + REGISTRATION EXTENDED!

Assalamu Alaikum, Dear Vendors,

We listened to your requests, and we’re making it easier for you to be part of the event! 🎉

🎁 50% DISCOUNT ON STALL PRICES

📅 Registration Extended to 10th September 2026

LIMITED SLOTS AVAILABLE - FIRST COME, FIRST SERVED!

This is your opportunity to showcase your products, connect with new customers, increase your brand visibility, and grow your business.

HOW TO SECURE YOUR SLOT

Join the official vendor registration group through the link below and submit your Expression of Interest (EOI).

👉 Registration link in Comment Section

Please note: Joining the group does not automatically guarantee a stall. Verified and shortlisted vendors will be contacted to proceed with payment and final registration.

Don’t wait until the slots are filled. Your next customer could be waiting for you at the Expo!

FIRST COME. FIRST SERVED.

"DUK WANDA YAKE JIN KUNYAR TALLAR TINUBU MUNAFIKI NE"Inji - RT. HON. Aminu Bello Masari (Tsohon Gwamnan Jihar Katsina)Ya...
16/08/2026

"DUK WANDA YAKE JIN KUNYAR TALLAR TINUBU MUNAFIKI NE"
Inji - RT. HON. Aminu Bello Masari (Tsohon Gwamnan Jihar Katsina)

Ya bayyana hakan ne a wajen taron Tinubu Dikko Assured 2027 na tallafawa malaman Islamiyya 690 da N30,000 Ko wane da kuma kaddamar da gyararrakin kewayuyyuka, azuzuwa da kuma rijiyoyin burtsatsai a Jihar Katsina.

OSUN 2026: ADEMOLA ADELEKE YA SAKE LASHE ZABEN GWAMNAN JIHARINEC ta ayyana Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord a ...
16/08/2026

OSUN 2026: ADEMOLA ADELEKE YA SAKE LASHE ZABEN GWAMNAN JIHAR

INEC ta ayyana Gwamna Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Jihar Osun na 2026, bayan ya doke abokin hamayyarsa na kusa, Bola Oyebamiji na APC.

Adeleke ya samu ƙuri’u 511,067, yayin da Oyebamiji ya samu 444,815, kamar yadda Jami’in Zaɓen INEC, Joshua Ogunwole, ya sanar a hedikwatar hukumar da ke Osogbo a safiyar Lahadi.

Sakamakon ya nuna cewa Adeleke ya samu rinjaye a ƙananan hukumomi 19 cikin 30, yayin da Oyebamiji ya lashe 11.

SAURAN SAKAMAKON ZAƁEN
Accord: 511,067
APC: 444,815
ADC: 17,180
AAC: 1,458
ADP: 2,946
APGA: 1,474
APM: 234
APP: 114
BP: 111
NNPP: 118
PRP: 83
SDP: 155
YPP: 534
ZLP: 2,482

Jimillar ƙuri’un da aka kada: 1,005,800
Ingantattun ƙuri’u: 985,079
Ƙuri’un da aka soke: 20,721.

Wannan nasara ta bai wa Adeleke damar ci gaba da jagorantar Jihar Osun bayan samun sabon wa’adi, yayin da sakamakon zaɓen ke ƙara jawo hankalin masu bibiyar siyasar Najeriya gabanin zaɓen 2027.

15/08/2026

Ana cigaba da bikin Chairman din karamar hukumar Katsina Isah Miqdad AD Saude

#

15/08/2026

DA DUMI DUMI: Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya gwangwaje shugaban hukumar Hisbah na Jihar Katsina Dr. Aminu Usman (Abu Ammar) da Sabuwar Mota.

14/08/2026

Yaushe Rawa ta bar kan mata ta koma kan maza?

Wane kasuwanci ne zaka iya farawa da naira miliyan daya, ya baka ribar naira dubu dari da ashirin duk wata?Idan kuma kan...
14/08/2026

Wane kasuwanci ne zaka iya farawa da naira miliyan daya, ya baka ribar naira dubu dari da ashirin duk wata?

Idan kuma kana kasuwanci ribar nawa zaka rinka samu akan naira miliyan daya idan aka kara maka ita a ciki?

12/08/2026

A halin yanzu a Nigeria wane abu ne zaku siya na naira dubu daya yayi maka sati kana cinsa?

MUTANE 28 DA SHUGABA TINUBU YABA MANYAN MUKAMAI A JIHAR KATSINAWa kuka fara gani a yau da muka wallafa? Su waye sukafi t...
12/08/2026

MUTANE 28 DA SHUGABA TINUBU YABA MANYAN MUKAMAI A JIHAR KATSINA

Wa kuka fara gani a yau da muka wallafa? Su waye sukafi taka rawar gani a cikin al’umma?

Hotunan su suna a comment section

1. Hannatu Musa Musawa – Ministar Al’adu, Yawon Buɗe Ido da Tattalin Arziƙin Ƙirƙire-ƙirƙire.

2. Muttaqa Rabe Darma – Ministan Gidaje da Raya Birane.

3. Ibrahim Kabiru Masari – Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa.

4. Dr. Aminu Maida – Shugaban Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC).

5. Tanimu Yakubu – Darakta-Janar na Ofishin Kasafin Kuɗin Tarayya (Budget Office of the Federation).

6. Aminu Bello Masari – Shugaban Kwamitin Amintattu na TETFund.

7. Dr. Badamasi Lawal – Babban Jami’in Gudanarwa na NSIPA.

8. Kabir Ibrahim Mashi – Kwamishinan Tarayya a RMAFC, mai wakiltar Jihar Katsina.

9. Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri – Shugaban AUDA-NEPAD Nigeria.

10. Badru Muntaka Ahmed – Babban Darakta mai kula da ayyukan noma na Sokoto-Rima River Basin Development Authority.

11. Abubakar Ibrahim Dutsin-ma – Babban Darakta mai kula da harkokin kuɗi na Sokoto-Rima River Basin Development Authority.

12. Hon. Fatuhu Mohammed Buhari – Darakta-Janar na National Agricultural Seed Council (NASC).

13. Ibrahim Shehu Shema – Tsohon Gwamnan Katsina, wanda aka ba muƙami a hukumar gwamnatin tarayya, ciki har da shugabancin kwamitin gudanarwa na Nigerian Shippers’ Council.

14. Sanata Kabir Abdullahi Barkiya – Shugaban Kwamitin Gudanarwa na NALDA.

15. Abdullahi Mohammed – Babban Darakta mai kula da harkokin gudanarwa da kuɗi na Nigeria-São Tomé and Príncipe Joint Development Authority.

16. Barr. Sama’ila Audu – Babban Darakta mai kula da harkokin gudanarwa na NSITF.

17. Karimah Bello – Babbar Darakta mai kula da harkokin talla na NTA.

18. Hon. Anas Isah Haruna – Kwamishinan Tarayya a Federal Character Commission, mai wakiltar Katsina.

19. Farfesa Idris M. Bugaje – Sakataren Zartarwa na NBTE.

20. Injiniya (Dr.) Sule Ahmed Abdulaziz – Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na TCN.

21. Sanata Ibrahim Ida – Shugaban Corporate Affairs Commission (CAC).

22. Farfesa Sadiq Isah Radda – Kwamishinan Tarayya a National Population Commission (NPC), mai wakiltar Katsina.

23. Manjo Janar Junaidu Sani Bindawa (mai ritaya) – Shugaban National Salaries, Incomes and Wages Commission (NSIWC).

24. Aisha Mahmud Kanti Bello- Commissioner at the Nigerian Electricity Regulatory Commission (NERC).

25. Maryam Idris Bagiwa – Daraktar Kasuwanci (Commercial Director) ta NNPCL.

26. Nasarawa Usman Mani – Mamba a Kwamitin Gudanarwa na Federal University of Health Sciences, Katsina.

27. Muhammad Abu Ibrahim — Sakataren Zartarwa kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Asusun Ƙasa na Bunƙasa Noma (NADF).

28. Ahmed Sodangi — Darakta-Janar na Gidan Kula da Ayyukan Fasaha na Ƙasa (National Art Gallery). ‎

29. Hadiza Bala Usman - Babbar Mai Ba Shugaban Kasa Shawara ta Musamman kan Daidaita Manufofi

30. Binta Adamu Bello - Darakta-Janar, Hukumar Kasa ta Hana Safarar Mutane (NAPTIP).

10/08/2026

“MU DAINA YAUDARAR KAN MU, TINUBU YA KAWO ALKHAIRI JIHAR KATSINA, MU NE BAMU BAKU BA”

Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, ya ce alheri da dama sun samu Jihar Katsina daga gwamnatin tarayya, sai dai abin da ya rage shi ne yadda ‘yan jihar za su yi amfani da damar da aka samar.

Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya bayyana haka ne yayin ganawa da ƙungiyoyi da masu ruwa da tsaki a Katsina, inda ya ce bai kamata a ɗora dukkan alhakin rashin samun ci gaba kan Shugaba Tinubu ba.

“Mu daina yaudarar kanmu. Alheri an kawo wa Jihar Katsina, mu ne ba mu ba ku ba,” in ji Alhaji Ibrahim Kabir Masari.

Ya ce idan aka bai wa ‘yan Katsina mukamai da dama a gwamnatin tarayya, alhakin waɗanda aka ba damar shi ne su tabbatar da cewa sun yi amfani da su wajen amfanar da jama’a.

Alhaji Ibrahim Kabir Masari ya kuma ambaci wasu ‘yan Katsina da ke rike da muhimman mukamai a gwamnatin tarayya, yana mai cewa irin waɗannan damar na daga cikin abubuwan da jihar ke samu.

Kalaman na Masari sun zo ne yayin da ake ƙara shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen 2027, inda APC a Katsina ta riga ta bayyana goyon bayanta ga Shugaba Tinubu da Gwamna Dikko Umar Radda.

Me kuke gani? Shin ‘yan Katsina na amfani da damar da suke samu a gwamnatin tarayya yadda ya kamata?

Address

Katsina
820221

Opening Hours

Monday 09:00 - 22:00
Tuesday 09:00 - 20:00
Wednesday 09:00 - 20:00
Thursday 09:00 - 20:00
Friday 09:00 - 16:00
Saturday 09:00 - 17:00
Sunday 09:00 - 17:00

Telephone

+2347086512580

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katsina Trends posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share