22/01/2025
Rundunar yan sanda ta jihar Katsina ta k**a mutanen da ake zargi da satar abun zuba shara (Container) mallakar hukumar kare muhalli ta jihar Katsina (SEPA) a Unguwar tudun Yarlehidda dake cikin garin Katsina.
Mutanen su biyar (5) da ake zargi yanzu haka suna hannun rundunar yan sanda ta jihar Katsina reshen sabon gari domin cigaba da gudanar da bincike.
Domin samun cikakken bayanai na sauran masu irin wannan mugun aiki da masu saye a cikin al'umma.
Hukumar ta kare muhalli ta jihar Katsina SEPA tana karkashin jagorancin shugaban hukumar Alh. Kabir Usman Amoga.