09/04/2026
An haifi Alhaji Abdulmumini Kabir Usman a ranar 9 ga watan Janairun shekarar 1952. Shi ɗa ne ga sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Kabir Usman, wanda shi kuma ɗa ne ga sarkin Katsina Usman Nagogo, shi kuma ɗa ga sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Dikko.
Karatu
Alhaji (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman, ya yi karatunsa na firamare a makarantar firamaren kwana (Dutsinma Boarding Primary School) ta Dutsinma, daga shekarar 1959 zuwa 1964. Daga nan kuma ya ci gaba zuwa makarantar sikandiren gwamnatin Katsina (Government Secondary School, Katsina) wacce daga baya ta koma kwalejin gwamnati ta Katsina (Government College Katsina), daga shekarar 1965 zuwa 1969. Bayan kammala wannan makaranta ya samu zarcewa zuwa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga shekarar 1972 zuwa 1974. A ƙarshe ya samu nasarar samun digiri a fannin soshiyoloji (Bachelor's Degree in Sociology) daga Jami’ar Ɗanfodiyo da ke Sakkwato.
Gogayyar Aiki
Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya zama Magajin Garin Katsina Hakimin Birni da kewaye lokacin yana ɗan shekara 30 a duniya. Yana kan wannan muƙami na Hakimin Birni da kewaye wanda a lokacin Katsina tana matsayin ƙaramar hukuma a Jahar Kaduna, sai aka ɗaukaka darajar Katsina zuwa jaha a shekarar 1987.
Ya riƙe muƙamai da dama, daga ciki akwai zamowarsa shugaban Jami’ar Oba-Femi Awolowo tun daga shekarar 2008 har zuwa 2015 inda aka canja shi zuwa shugabancin Jami’ar Ilorin.
Ya yi aiki a matsayin chairman na wasu ƙungiyoyi da ma’aikatun gwamnati da hukumomi da aka yarda cewa sun haura 71.
Zamowarsa Sarki
A ranar 13 ga watan Maris na shekarar 2008 aka ayyana sunan Alhaji (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman a matsayin sarkin Katsina, bayan da masu zaɓen sarki s**a zaɓe shi a matsayin sabon sarkin Katsina bayan rasuwar mahaifinsa Alhaji Muhammadu Kabir Usman. An yi bikin naɗinsa aranar 5 ga watan Yuli na shekarar 2008.
Gudunmawar da Yake Bayarwa
Mutum mai son jama’a da kuma yi musu hidima kamar Alhaji (Dr.) Abdulmumini Kabir Usman, abu ne mai wuya a iyakance irin gudunmawar da yake baiwa jama’a. Alƙaluma sun kasa ƙididdige ɗimbin mutanen daya ya samawa guraben karatu a jami’o’in ciki da wajen Najeriya.
Sakamakon irin ayyukan taimakon al’umma da yake yi, ya samu kyaututtuka na girmamawa, kamawa tun daga ƙaramar hukumar Katsina, har zuwa matakin jaha har zuwa matakin tarayya inda aka bashi lambar yabo mai taken “Commander of the Federal Republic (CFR)”.
Gobe In Allah ya yarda next