07/04/2026
Ƙungiyoyin Al'umma musamman na Matasa daga Ƙaramar Hukumar Ƙafur na cigaba da kiranye ga Engr. Abdulaziz Kabir Abdullahi da ya fito Kujerar Ɗan Majalissar Dokoki ta Jiha mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Ƙafur a zaɓen shekarar 2027 dake tafe.
Ƙungiyoyin sunyi wannan kira ne ga Engr. Abdulaziz Kabir Abdullahi duba da irin ƙoƙari da ɗawainiya da yake yi da al'ummar Ƙaramar Hukumar Ƙafur, shine s**a ga ya dace ya fito wannan kujera.
Domin cigaba da kawoma al'ummar Ƙaramar Hukumar Ƙafur abubuwan cigaba kamar yadda yakeyi a yanzu, sanin kowa ne musamman al'ummar Ƙaramar Hukumar Ƙafur Engr. Abdulaziz Kabir Abdullahi yayi fice.
Wurin taimakon al'umma ta kowane fanni wanda ya ƙunshi harkokin ilimi, kiwon lafiya, tallafama matasa da mata da marayu da dai sauran su.
Da wannan muke ƙara kira gareshi da ya fito wannan takara domin al'ummar Ƙaramar Hukumar Ƙafur na buƙatar wakilcin sa a zauren Majalissar Dokoki ta Jihar Katsina.
Sako daga gamayyar Ƙungiyoyin Matasa masu son cigaban Ƙaramar Hukumar Ƙafur.