29/07/2024
'YAN SIYASA SUNA KARA ZUBAR DA KIMAR RUNDINAR SOJIN NIGERIA
Jiya Babban Supeta janar na 'yan sandan Nigeria yace zasu bawa masu zanga-zanga kariya matukar ta lumana ce
Yau kuma sanarwa daga Babban Hafshin Sojojin Nigeria yace ba zasu bari masu zanga-zanga su wargaza kasa ba (amma kuma an bari 'yan ta'adda suna cigaba da wargaza mana kasa ai) abin kunya kawai
Abu na farko: Zanga-zanga ba laifi bane a tsarin mulkin Demokaradiyya, kuma ya zama wajibi ga 'yan sanda su bawa masu zanga-zanga kariya kamar yadda yake a doka
Abu na biyu: Rundinar 'yan sandan Nigeria ita ne wanda kundin tsarin mulkin Kasa na Constitution ya daura mata alhakkin kula da harkokin tsaron cikin gida, sai idan lamarin tsaron cikin gida yafi karfinta kafin nan sai Sojoji su kawo mata agaji
Idan an fahimci wannan, to bai kamata rundinar Sojin Nigeria tayi wannan gargadi ga masu shirya zanga-zanga ba domin ba huruminta bane, zanga-zanga civil matter ne, sam bai kamata a shigo da Sojoji ba cikin wannan hayaniya
Yanzu da Sojoji s**a fitar da wannan sanarwa, sai kuma ya kasance masu zanga-zanga sun fito, shin hakan ba zubar da kima da kwarjinin rundinar Sojin Nigeria bane?
Ko da wasa bai kamata rundinar Sojin Nigeria ta bari 'yan siyasa suna rage mata mutunci da daraja ba a idon 'yan kasa saboda biyan bukatun 'yan siyasar, wannan yana kara dagula harkokin tsaron kasa gaba daya
Ita rundinar Sojin Nigeria itace rundina mafi karfi, an samar da ita ne don tayi yaki ta kare Kasa ta sama da kasa da ruwa daga mahara ketare ko kasashen waje, itace last hope a fannin tsaro, shiyasa bai kamata soja yayi mu'amala da fararen hula ba
Kuma bai kamata Soja ya shiga harkokin tsaron cikin gida ba, domin ba akan haka ya samu horon aiki ba, abinda aka horar da Soja shine yayi harbi ya kashe abokin gaba, 'yan sanda kuma aikin su shine su kare rayukan 'yan kasa da dukiyoyinsu, sannan suyi bincike kan masu aikata laifuka
Amma abin takaici yau mun wayi gari miyagun 'yan siyasa sun lalata mana rundinar Sojin Nigeria,