12/04/2026
SHIN WAYOYINMU SUNA LEKEN ASIRINMU NE?
GA GASKIYAR ABIN DA KE FARUWA! 📱👁️
Sau da yawa idan mun zauna muna hira da aboki akan wani abu, ko kuma munyi tunanin siyan wani abu, muna hawa social media sai mu ga tallan abun ya bayyana a Facebook ko Instagram.
Mutane da yawa na tunanin wayar tana jin abin da muke fada ko kuma tana mana leken asirine😅.
Gaskiyar magana ita ce, kamfanonin fasaha kamar kamar irinsu Meta da Google sun wuce duk yanda muke tunani. Ba sa bukatar sauraron muryarka domin suna da hanyoyin da s**afi wannan na bin sawunka.
Ga yadda hakan ke faruwa dalla-dalla:👇🏽👇🏽
1. AKWAI ABINDA AKE KIRA, DIGITAL PIXELS & COOKIES 🍪
Duk lokacin da ka ziyarci wani website ko ka yi bincike (search) a Google, akwai wasu ƙananan bayanan sirri da ake kira "Cookies" da ke biye da kai.
Idan ka duba farashin "Clipper" a wani shafi, wannan shafin zai sanar da Facebook cewa IP Address kaza yana son clipper. Kana komawa Facebook, sai kafara cin karo da wadannan tallan.
2. SANNAN AKWAI DATA INTEGRATION 🤝
Kamfanin Meta shi ya mallaki Facebook, Instagram, da WhatsApp.
Idan kayi hira a WhatsApp dukda tsaron da yake dashi, bayanan abubuwan da kake yawan magana kansu ko links din da kake dannawa suna taimaka wa Facebook wajen gano abin da kake sha'awa, nanma kana dawowa sauran media dinka zaka fara cin karo dasu.
3. AKWAI KUMA LOCATION & PROXIMITY📍
Wannan shi ne babban dalilin da ya sa kake ganin mutanen da ka hadu da su a People You May Know.
Idan kai da wani abokinka kuka zauna a guri daya na tsawon lokaci, wayoyinku suna sanar da server cewa kuna tare ta hanyar GPS ko Bluetooth,
Facebook zai yi tunanin tunda suna tare, tabbas sun san juna. Shi ya sa kake ganin tallan abin da abokinka ya duba a wayarsa. Hakan ya nuna bawai iya abinda kai kake mu'amala dasubane harda wanda abikinka ke yawan dubawa musamman idan kuna zama wuri daya, "Abokin Barawa Barawome" 😂 Inji Hausawa.
4. SANNAN AKWAI PREDICTIVE ALGORITHMS 🧠
Wannan wata fasahar Artificial Intelligence (AI).
Kamfanonin nan sun riga sun san halayenka. Sun san shekarunka, inda kake zama, da irin abubuwan da mutane kamarka suke so.
Idan kowa a unguwarku yana maganar "Taki," AI zai hasashen cewa kai ma kana bukata, sai ya fara nuna maka tallan tun kafin ma ka yi tunaninsa.
5. SANNAN AKWAI LOOKALIKE AUDIENCES 👥
Masu talla suna amfani da wani abu da ake kira "Lookalike Audiences." Idan dubban mutane masu ra'ayi irin naka sun sayi wani abu, Facebook zai nuna maka wannan abun domin ya san kai ma kana da wannan dabi'ar. Misali kai graphic designer ne, sekuma a area din da kake graphic designers dayawa s**a siya mouse na computer within short range of time, to kaima koda baka nemaba akwai yiwuwar kafara ganin tallukan a wayarka.
YANDA ZAKA KAUCEWA KO RAGE FARUWAR HAKAN:
Idan baka son hakan tadinga yawan faruwa dakai, ga abin da zaka yi:
Ka shiga Settings na Facebook dinka, ka duba Off-Facebook Activity sannan ka goge shi (Clear History).
Ka kashe Location Services a apps din da baka bukata.
Karka ba kowane App damar shiga cikin Contacts ko Microphone dinka idan ba yakama doleba.
Ba sihiri ba ne, kuma ba wai lallai ana sauraron maganarka ba ne😊
lissafi ne na na'ura (Mathematics & Data).
Muna rayuwa ne a duniyar da Bayanai (Data) tazama kadara mai tsadar gaske.
Shin kai ma hakan ta taba faruwa da kai? Ka taba maganar wani abu sai ka ganshi a Facebook? Fada mana a comment!👇
Umar Mukhtar Abba ✍🏽
10/04/2026