07/09/2025
,,Hmmm ga hadin da idan kk rikeshi, duk kunhuta da wata dilka domin shi kafi dilka ne zai gyaraki ya cire maki matacciyar fata kiyi kyau kina walkiya, haske da annuri π idan kinada pimples zai cire,ko gishirin hanci ,kunar Rana, dabbareΒ² dss ku gwada wannan sirrin tested and trusted πne
Garin lalle 1tbsp
Garin ganyen magarya 1tbsp
Garin kurkur 1tbsp
Garin camwood (majigi) ana samu wajen yan koli 1/2tbs
Garin bawon lemun zaki 1tbsp
Sabulun pharmadem kashi daya bisa uku 1/3
Sabulun dove kashi daya bisa hudu 1/4
Ruwa kamar ledar pure water daya 50cl
Zuma 2tbsp
Lavender oil 5ml
Tea tree oil 5 drop
Neem oil 5 drop amma da na company
Vitamin E 2 capsule
Manja 1tbsp
Man kwakwa 15ml
Kisamu kwano na silver kizuba ruwa ki kawo duka garukan nan ki zuba a ciki ki juya kidora bisa wuta kirage wutar kasa harya tafarfasa amma kina kusa don karya taso ya sheke kasa! Idan ya dahu saiki sauke dama kin gurza sabulan ki saki kawo ruwan maganin nan kisa kwando kitace a kan sabulun kimotsa ki rufe harsai ya narke
Idan sabulun ya narke, saiki kawo duka sauran kayan kizuba su cikin hadin sabulun ki motsa kizuba preservative 2-3drop kijuya kisamu roba me murfi kijuye abunki idan kunason lemun tsami zaku iya sakawa 15ml na ruwan shi da yamma kishafa a fuska kina massaging duk kishafeta da wannan hadin yaji saiki barta kamar 30mnt kisa soso me laushi kiwanke saiki kawo manki maikyau kishafeta
To tun a rana ta farko ma saikinga canji a fuskarki ba saka shi a shiga rana kina iya yi sau biyu a rana za kuma ki iya maidashi sabulun fuskarki
Fatana dukwacce ta gwada shi taji dadi tamun addu'a Allah biyamun bukatuna na alkhairi dani daku baki daya ya gafarta mana zunaban mu Kuma yasa muyi kyakykyawan karshe