16/02/2026
🌙✨ SANARWAR GAYYATA
ZUWA BUƊE TAFSIRIN ALƘUR’ANI NA RAMADAN ✨🌙
Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin ƙai.
Markaz-Thaqafaul Islamiyya Toro tare da ɗaliban Malam suna farin cikin gayyatar al’umma baki ɗaya zuwa Buɗe Tafsirin Alƙur’ani Mai Girma na watan Ramadan.
Za a fara tafsirin ne da yardar Allah a yau Litinin bayan Sallar Isha’i, ƙarƙashin jagorancin malaminmu:
IMAM ALIYU AHMAD SAMBO
(NAIBI II CENTRAL MOSQUE FADAN TORO)
Wannan wata dama ce ta musamman domin ƙara kusanci da Alƙur’ani, fahimtar ma’anoninsa, da samun shiriya da falala a wannan wata mai albarka.
Allah Maɗaukaki Ya ce:
"شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ هُدًى لِلنَّاسِ"
“Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Alƙur’ani a cikinsa, shiriya ga mutane…” (Al-Baqarah: 185)
Muna kira ga Al'ummah, matasa da manya da su halarta domin amfana da wannan tafsiri mai albarka.
📍 Wuri: Central mosque fadan Toro
🕰 Lokaci: Yau Litinin, bayan Sallar Isha’i
Allah Ya sa mu kasance cikin masu sauraro da aiki da abin da muka ji.
Sanarwa daga:
Markaz-Thaqafaul Islamiyya Toro
🌙 Ramadan Kareem 🌙