23/11/2025
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
Zamfara SOCU - Social Register Update & NIN Integration na sanar da al’ummar Jihar Zamfara cewa ya zama wajibi kowane ɗan ƙasa ya mallaki Katin Shaidar Dan kasa (National Identification Number- NIN).
Saboda haka, jami’an SOCU za su zagaya lungu da sako a dukkan kananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara domin:
tattara bayanan masu NIN,
sabunta rajistar al’umma masu ƙaramin ƙarfi,
da tabbatar da cewa duk wanda ya cancanta ya shiga cikin bayanan tallafin gwamnati.
Aikin kyauta ne gaba ɗaya.
Ba a yarda wani ma’aikaci ya karɓi ko sisin kwabo daga kowa ba. Don haka ana roƙon al’umma su ba da cikakken haɗin kai tare da yin hattara da duk wani mai yaudara ko ɓataci yayin gudanar da aikin.
Mun gode da haɗin kai da fahimtar ku.