GIWA TV

Call Directions Contact the business

GIWA TV Kafar Zamani Domin Shiri Kai Tsaye, Labarai da Rahotanni, Karatun Addini da Tallace Tallace Kana mu Nishadantar da Masu Bibiyan Shafukan mu na Yanar Gizo.

Zaku iya Samun mu a 08064418179. Mungode!!!

13/09/2026

Mauludin Zawiyyar Sheikh Alaramma Isma'il Imam Misau da aka Saba Gudanarwa duk Shekara

Nan wani Babban Masallaci ne a garin Misau.Daga ina aka tsaya aka dauki wannan hoton. Sannan akwai darasi a cikin Hoton,...
13/09/2026

Nan wani Babban Masallaci ne a garin Misau.
Daga ina aka tsaya aka dauki wannan hoton. Sannan akwai darasi a cikin Hoton, Miye ne ?

13/09/2026

Tawagar Shehu Kawai Karkashin Jagora Hon. IIbrahim Makama Ta K**a Hanya Zuwa Bauchi Taron Jam'iyar PRP

Rana ta biyu K**ar jiya yauma ansake fita domin sallan rokon ruwa a masallachin izala dake water board kan hanyar hardaw...
13/09/2026

Rana ta biyu

K**ar jiya yauma ansake fita domin sallan rokon ruwa a masallachin izala dake water board kan hanyar hardawa

BASKO GIDA GIDA MEDICAL OUTREACH DA MOBILIZATION A AJILIA yau, 12 ga Satumba, 2026, ƙungiyar Basko Gida Gida Medical Out...
12/09/2026

BASKO GIDA GIDA MEDICAL OUTREACH DA MOBILIZATION A AJILI

A yau, 12 ga Satumba, 2026, ƙungiyar Basko Gida Gida Medical Outreach and Mobilization ta gudanar da rabon magunguna, gwaje-gwaje da duba marasa lafiya kyauta a garin Ajili, ƙarƙashin jagorancin Haj. Binta Abba Garo, mai ɗakin Hon. Basko Mangari.

A jawabinsa, Shugaban ƙungiyar, Mal. Nazeef, ya yaba matuƙa ga Hon. Abba Garo, ɗan takarar Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar Chiroma District a ƙarƙashin jam’iyyar APC, tare da mai ɗakinsa Haj. Binta Abba Garo, bisa wannan kyakkyawan aikin alheri da suke gudanarwa domin tallafawa al’umma.

Shi ma Alh. Zagi Mohammed CNA, wanda ya yi jawabi a madadin amininsa Hon. Abba Garo, ya bayyana wa al’ummar Ajili cewa, “Ku ’yan gida ne tun kafin siyasa.” Ya ƙara da cewa bayan Mangari, Ajili ita ce second home dinsu, kuma dangantakarsu da al’ummar Ajili ba ta fara da siyasa ba.

Alh. Zagi ya kuma roƙi al’ummar Ajili da su ci gaba da ba su goyon baya, tare da neman alfarmar ƙuri’unsu a ranar zaɓe, idan Allah Ya kai su wannan rana.

A nata jawabin, jagorar ƙungiyar, Haj. Binta Abba Garo, ta gode wa ma’aikatan ƙungiyar bisa jajircewarsu, tare da miƙa godiya ta musamman ga al’ummar Ajili bisa kyakkyawan haɗin kai da s**a bai wa ma’aikatan, da kuma yadda s**a fito kwansu da kwarkwatarsu domin amfana da shirin.

Ta kuma roƙi al’ummar Ajili da su ma, a ranar zaɓe, su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaɓar jam’iyyar APC.

An kammala taron da addu’ar fatan alheri, tare da roƙon Allah Ya saka wa dukkan waɗanda s**a bayar da gudummawa da alheri, Ya kuma ƙara haɗa kan al’umma.

12/09/2026

Sake Kaddamar Da Kungiyar Misau Practical feild Fadama Farmers Da Karrama Daya Daga Cikin Members NataWanda Aka Bashi Coordinator Na Kukadi Word Mamman Na Ado

AN SAKE GABATAR DA SALLAR ROKON RUWA A GARIN BASIRKA 🤲Yau, Al’ummar garin Basirka da ke Darazo LGA, Jihar Bauchi, sun sa...
12/09/2026

AN SAKE GABATAR DA SALLAR ROKON RUWA A GARIN BASIRKA 🤲

Yau, Al’ummar garin Basirka da ke Darazo LGA, Jihar Bauchi, sun sake gabatar da Sallar Rokon Ruwa (Salatul Istisqa’i) a babban Masallacin Idi, domin neman rahamar Allah da ruwan sama mai albarka.

Muna roƙon Allah SWT cikin sunayensa kyawawa da siffofinsa madaukaka, Ya shayar da mu ruwan sama mai amfani, ba mai cutarwa ba. 🌧️🤲

Ya Allah, Ka sanya ruwan sama ya zama albarka ga gonakinmu, ciyarwa ga dabbobinmu, da rahama ga al’ummarmu. Ka wanke mana zunubanmu, Ka gafarta mana kura-kuranmu.

Ya Allah, Ka shayar da mu! Kai ne Mai juya al’amura, kuma babu mai iya kawo mana ruwa sai Kai.

🤲 اللهم أغثنا، اللهم أغثنا، اللهم أغثن

Allahumma Aghithna! Ya Allah Ka kawo mana agaji da ruwan sama.

📍 Basirka, Darazo LGA, Bauchi State.

DANDANZON AL’UMMAR GARIN MISAU SUN FITA SALLAR ROƘON RUWADandazon al’ummar Garin Misau sun fito domin gudanar da Sallar ...
12/09/2026

DANDANZON AL’UMMAR GARIN MISAU SUN FITA SALLAR ROƘON RUWA

Dandazon al’ummar Garin Misau sun fito domin gudanar da Sallar Roƙon Ruwa (Salatul Istisqa’i) a Masallacin Izalah da ke Water Board, Misau, domin roƙon Allah Maɗaukakin Sarki Ya saukar mana da ruwan sama mai albarka.

Allah Ya amshi addu’o’inmu, Ya saukar mana da ruwan sama mai amfani, Ya sanya shi rahama da albarka ga ƙasa da al’ummar Misau baki ɗaya. 🤲

Amin Ya Rabbal Alamin.

Address

Sabon Layi Street Misau

Telephone

+2348064418179

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when GIWA TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to GIWA TV:

Share